Jihohin Amurka 17 sun kai gwamnatin Trump kara

Undocumented immigrant families are released from detention at a bus depot in McAllen, Texas Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu iyayen da ak saki daga wani sansanin gwamnatin Amurka a McAllen na jihar Texas

Jihohin Amurka 17 ne suka kai karar gwamnatin Donald Trump akan abin da suka kira mugunyar hanyar da ta ke bi na raba 'ya'yan mutanen da suka shiga Amurka ba tare da izini ba da iyalansu.

Jami'an gwamnatoci masu shigar da kara jihohin da suka hada da Washingtin da New York da California ne suka shigar da karar ta hadin gwuiwa, kamar yadda zakuji a wannan rahoton da Sani Aliyu ya hada mana.

Wannan karar na neman dakatar da shirin gwamnatin Amurka na hana masu neman mafaka shigakasar ta kan iyakar Amurka da kasar Mexico.

Tun da farko, mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya gargadi masu son shiga kasar da su sani cewa za a iya raba su da 'ya'yansu idan suka cigaba da kokarinsu na shiga kasar.

Jihohin Massachusetts, Delaware, Iowa, Illinois, Maryland, Minnesota, New Jersey, New Mexico, North Carolina, Oregon, Pennsylvania, Rhode Island, Vermont da Virginia har da District of Columbia ne sauran jihohin da suka shigar da karar a wata kotu da ke birnin Seattle na jihar Washington. Kuma sun bayyana sabon umarnin Mista Trump na daina rana yara da iyayensu a matsayin wani mafarki.

Jihohin na kuma neman kotun ta umarci gwamnatin ta Amurka da ta daina raba yara da iyalansu, kana ta bayyana matakin a matsayin wanda ya taka tsarin mulki.

Ofishin da ke kula da samar wa 'yan gudun hijira matsuguni na gwamnatin Amurka ya tabbatar da cewa akwai yara 11,800 da hukumar ke rike da su a wurare daban daban cikin Amurka, kuma yawancinsu kananan yara ne da iyayensu suka tura su zuwa Amurka ba tare da wani babba da ya raka su ba.

Wannan kara dai ta yi kama da karar da aka shigar akan batun nan na hana Musulmai shiga Amurka, wanda wata karamar kotu a Hawaii ta ce laifi ne, amma daga baya babbar kotun Amurka ta amince da matakin.

Labarai masu alaka