Alkalin kotun kolin Poland ta ki sauka daga mukaminta

Malgorzata Gersdorf branded the move to make some judges retire early as a "purge" Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Malgorzata Gersdorf ta ce matakin korar alkalan kasar haramtacce ne

Shugaban kasar Poland Andrey Dudaza zai kori babbar alkalin kotun kolin kasar daga mukaminta a yau Talata, inda zai maye gurbinta da wani na hannun damansa.

Kuma daga yau ne wata doka da za ta rage tsawon shekarun aikin alkalan kasar daga 70 zuwa 65, amma Tarayyar Turai ta soki shirin

Tun da farko wani mai ma shugaban kasar hidima ya ce dole ne alaklin alkalan babbar kotun mai shekara 65 da haihuwa, Malgorzata Gersdorf ta sauka daga mukaminta.

Amma wani kakakin kotun kolin ya ce alkalin za ta bijire ma wannan umarnin, kuma za ta koma bakin aikinta a gobe Laraba.

Ta kuma ce wannan matakin haramtacce ne saboda kundin tsarin mulkin kasar Poland ya tabbatar mata da wa'adin alkalancinta har zuwa shekarar 2020.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty

Jam'iyyun siyasa masu adawa da gwamnatin kasar na shiry wata zanga-zanga a gaban kotun kolin kasar domin nuna goyon bayansu gareta.

Tun da ta dare bisa karagar mulki, jam'iyya mai mulki a Poland ta fitar da wasu dokoki da zummar kallafa ikonta akan kotunan kasar.

Kuma gwamnatin ta ce matakan nata na da muhimmanci saboda a tace tsofaffin alkalai da suka yi ma kasar illa tun daga lokacin mulkin kwaminisanci.

Labarai masu alaka