Syria: 'An kashe dan Abu Bakr al-Baghdadi'

Abu Bakr al-Baghdadi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rabon da a ga Abu Bakr al-Baghdadi tun 2014

Kungiyar mayakan IS ta ce an kashe Hudayfah al-Badri dan shugabanta, Abu Bakr al-Baghdadi a wani hari da aka kaddamar a Syria.

Kafar yadda farfagandar kungiyar ta Amaq ta ce an kashe shi ne a wani hari da aka kai, kan wata cibiyar wutar lantarki da ke birnin Homs.

Babu wanda ya san inda mahaifinasa Baghdadi ya ke, sai dai kalaman da aka yi amfani da su wajen fitar da sanarwar mutuwar na nuna alamomin yana raye.

An dai sha bayar da rahotannin mutuwar Al-Baghdadi wanda a 2014 ya kaddamar da hare-hare a arewacin Iraqi.

Labarai masu alaka