Isra'ila na son rusa kauyen Falasdinawa

Adnan Husseini Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Babban jami'in hukumar Falasdinawa Adnan Husseini

Tashi-hankali ya barke a gabar yamma na kogin Jordan da ke karkashin ikon Isra'ila saboda wani shiri na rusa wani kauyen Falasdinawa.

A watan Mayu ne dai kotun kolin Isra'ilar ta amince da a tashi kauyen daga wurin domin yana tsakiyar wasu matsugunai biyu na Yahudawa.

'Yan sanda masu kula da tsaro a kan iyaka sun hana Adnan Husseini, wani babban jami'in hukumar Falasdinawa, shiga kauyen, lamarin da ya janyo tashin hankali har 'yan sandan suka kayar da shi a kasa.

Kungiyar Red Crescent mai ayyukan bayar da agaji ta ce akalla mutum 35 ne suka sami rauni a wannan rikicin.

Ta kara da cewa kauyen mallakin Falasdinawa fiye da 180 ne da suka shafe fiye da shekaru 60 a yankin.

Magoya bayansu sun ce wannan matakin na gwamnatin Isra'ila ba komai ba ne illa wani kokari na batar da jinsin Falasdinu daga yankin baki daya.

Kotun kolin Isra'ila ce ta bayar da umarnin rusa kauyen, kuma gwamnatin kasar ta ce Falasdinawan ba su da izinin zama a yankin domin haka za ta mayar da su wani yankin.

Amma Falasdinawa sun ce Isra'ila bata taba bayar da irin wannan takardun izinin ba a shekarun baya.

Wannan kauyen na kan wata muhimmiyar hanya ce a tsakiyar yankin yammacin kogin Jordan dab da babbar mashigar birnin Kudus.

Labarai masu alaka