Austreliya: An dakatar da kamfani saboda muzguna ma tumaki

Sheep Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani kamfanin kasar Australia ya fada cikin wata rigimar kasuwanci da ya janyo aka hana shi fitar da dubban raguna da tumaki zuwa kasashen Larabawa.

Tun da farko kamfanin ya fuskanci hukuncin gwamnatin kasar bayan an same shi da laifin rashin tausaya ma dabbobi.

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Austreliya ce ta soke lasisin kamfanin Emanuel Exports da ke birnin Perth na kasar saboda samunsa da aka yi da laifukan azabta ma dabbobi.

Saboda haka ne ma kamfanin ya nemi ya yi amfani da wani reshensa don fitar da dabbobi zuwa kasar Kuwait.

Gaba daya kasuwar dabbobin kasar ta fuskanci matsi bayan da fiye da dabbobi 2,000 suka mutu a cikin wani jirgin ruwa mallakin kamfanin na Emanuel Exports.

A wani bidiyo da masu fafutukar kare hakkokin dabbobi suka nada, an ga daruruwan tumaki na kwance male-male cikin zawonsu, inda suka yi ta mutuwa saboda tsananin zafi a yayin da ake kokarin kai su yankin gabas ta tsakiya.

Wannan ne ya sa gwamnatin Austreliya ta sake duba matakan kiwon lafiyar dabbobi a kasar.

Labarai masu alaka