Bincike: Masu cutar Ebola na samin tabin hankali

Ebola Health Workers

Masu bincike a kasar Saliyo sun gano cewa wadanda suka yi jinyar cutar Ebola na fama da wani ciwo da ya kan shafi kwakwalwa na lokaci mai tsawo bayan sun warke daga cutar.

Akwai kuma shaida mai karfi da ke nuna cewa ba a warkewa gaba daya daga cutar.

An dai wallafa wannan binciken a mujallar Emerging Infectious Diseases.

A lokacin da ake gudanar da wannan binciken, an ware wadanda aka lura suna da alamun ciwon tabin hankali, wadanda a baya suna cikin 'yan kasar Saliyo da suka yi fama da cutar Ebola.

Masu bincike daga jami'ar Liverpool da makarantar Kings College ta birnin Landan sun gano cewa yawancinsu na fama da matsanancin ciwon kai da shayewar jiki kuma sun shiga wani halin damuwa mai zurfi.

Wadda ta jagoranci binciken mai suna Post Ebola Syndrome Project, Dokta Janet Scott ta yi kira da a horas da ma'aikatan jinya sosai akan yadda za su iya gano wannan matsalar.

Fiye da mutum 11,000 suka mutu daga cutar Ebola kuma akalla mutum 28,000 ne aka bayyana cewa sun kamu da cutar a Saliyo da Laberiya da kasar Guinea a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2016.

Wannan binciken ya tabbatar da bukatar da ake da ita ta a fadada bincike akan tasirin cutar Ebola na lokaci mai tsawo saboda yawan wadanda suka warke daga cutar na da yawa a yankin Afirka ta Yamma.