Jami'an lafiya na yajin aiki a New Zealand

Health workers Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kusan jami'an lafiya 30,000 ne suka tafi yajin aiki kan rashin biyansu albashi a kasar New Zealand.

Wannan ne karon farko cikin shekara 30 da suka taba daukar matakin irinsa kan batun albashi.

Kungiyoyin kwadago da ma'aikatar lafiya sun dauki dogon lokaci suna jani-in-ja kan batutuwan biyan albashi da walwalar ma'aikata amma hakan ba ta samu ba dole suka tafi yajin aikin.

Firai ministan rikon kwarya Winston Peter ya bayyana cewa lamarin ya bashi kunya bai kuma tsammaci hakan za ta faru ba.

A bangare guda kuma shugabannin kwadago sun yi alkawarin ba za su bari rayuwar marasa lafiya ta shiga hadari ba sanadiyyar yajin aikin.

Labarai masu alaka