Turkiyya ta soke dokar ta-baci

Recep Tayyib Erdogan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan

Gwamnatin Turkiyya ta dage dokar ta baci da ta fara aiki shekara biyu da suka gabata saboda yunkurin jurin mulkin da aka yi ma Shugaba Erdogan.

Dokar ta fara aiki ne bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

A karkashin dokar ta bacin an kama dubban mutane a kasar, kuma wasu dubban sun rasa ayyukansu.

Amma yanzu gwamnatin kasar ta fasa sabunta dokar bayan da ta yi haka har sau uku a baya.

Wannan matakin ya biyo bayan nasarar da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya samu a zaben shugaban kasa da ya gudana a makonnin baya.

A yayin yakin neman zaben da aka yi, wasu 'yan takara sun yi alkawarin soke dokar da zarar sun sami nasarar lashe zaben.

Fiye da mutum 107,000 aka kora daga aiki kuma fiye da mutum 50,000 aka tsare a kurkuku inda suke jiran a yi masu shari'a.

Gwamnatin Turkiyya ta zargi yawancin wadanda ta kora daga aiki da zama magoya bayan wani malamin addinin Islama, Fethullah Gulen, wanda a halin yanzu ke gudun hijira a Amurka, kuma a da abokin tafiyar siyasa ne ga Mista Erdogan.

Gwamnatin Mista Erdogan ta dade tana zargin malamin addinin da magoya bayansa da laifin shirya juyin mulkin, amma ya musanta haka.

Kokarin juyin mulkin na 2016 ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 250 bayan da wani jirgin yaki ya kai harin bam akan majalisar kasar.

Labarai masu alaka