'Dan sanda ba abokin gaba bane'

Nigeria Police on duty
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Sha'anin tabarbarewar tsaro ya ci gaba da sanya damuwa a Najeriya, har wasu kungiyoyin dattijai sun gudanar da taron nufin lalubo hanyoyin magance wannan al'amari.

Wasu dai na ganin matsalar ta samo asali ne sakamakon rikon sakainar kashi da aka yi wa aikin 'yan sanda tsawon lokaci.

Rahotanni sun ce ana samun korafe-korafe na rashin biyan hakkokin aiki a kan lokaci da kuma rashin bai wa rundunar 'yan sandan isassun kudin da za ta tunkari kalubalan tsaron da ke tasowa.

Mallam Sulaiman Abba, tsohon babban sufeton 'yan sanda ne, kuma ya gabatar da mukala yayin taron.

Ya kuma shaidawa BBC daya daga cikin matsalolin da suke janyowa aikin dan sanda mummunanr fahimta shi ne rashin jituwa tsakanin su da al'umar da suke karewa.

''Shekaru da dama da suka gaba a matsayi na ma'aikacin 'yan sanda da ke tasre dukiyar al'uma, ina ganin abin da ya janyo lalacewar aikin dan sanda shi ne rikon sakainar kashi da ake yi wa aikin."

Ya kara da cewa: "Tsarin mulki ya bai wa dan sanda damar kare jama'a da dukiyarsu. Sai da aka fadi dan sanda kafin wani.

Ya kuma ce, "Dokoki sun bayyana aikin dan sanda shi ne kama masu laifi ta hanyar bincike da gurfanar da su gaban kotu bi sa umarnin mai gabatar da kara na gwamnati''.

Hakkin mallakar hoto Audu Marte
Image caption Wasu 'yan sandan Najeriya sun yi zanga-zanga a Maiduguri a kwanan baya

Malam Sulaiman ya kara da cewa,''Amma abin mamaki sai ya kasance babu jituwa tsakanin 'yan sanda da wadanda ya kamata ya tsare. Daman kullum wanda ake cuta ba shi da abokin gaba sai mai cutarsa''.

Ya shaidawa BBC Hanyar da ya kamata abi dan magance matsalar ta hanyar bai wa 'yan sanda kayan aiki na zamani, da tabbatar da ba su horo dan su kware a aikinsu.

A debi mutane aiki yadda ya kamata, duk wanda bai yi aikinsa yadda ya dace ba to a hukuntashi da raba shi da aikin hakan zai sanya a rage matsalolin tsaro.

Haka kuma samari da 'yan mata da suka gama karatu su samu ayyukan yi, ba lallai sai na gwamnati ba ko daga hukumomi masu zaman kansu ta hakan za a rage zaman banza da ke kawo yaduwar aikata muggan laifuka tsakanin al'uma.

Labarai masu alaka