Cuba za ta yi sauyi ga tsarin mulkinta

Miguel Diaz-Canel Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Miguel Diaz-Canel na Cuba

Sabuwar majalisar kasar Cuba ta fara zama a karon farko domin yin sauye-sauye ga tsarin mulkin kasar.

Ana sa ran mika sakamakon tattaunawar ga 'yan kasar domin su kada kuri'ar raba gardama a kai.

A karkashin sauye-sauyen da majalisar ke sa ran gabatarwa, akwai batutuwan ba 'yan kasar ikon mallakar dukiya a karon farko.

Ana kuma sa ran a kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa da amincewa da auren jinsi.

Wannan ne zaman farko na majalisar Cuba tun bayan da aka zabe su a watan Afrilu, kuma babban aikin da ke gabansu mai cike da tarihi ne.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar kasar Cuba

A cikin batutuwan da ke gaban majalisar akwai na sabunta tsarin mulkin kasar na 1976 domin shigar da sabbin gyare-gyare da aka samar ta bangaren tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar.

Mafi muhimmanci a cikinsu shi ne batun ikon mallakar dukiya da za a bai wa 'yan kasar.

Raul Castro wanda shi ne shugaban jam'iyyar kwamunisanci ta Cuba - wanda kuma ya mika ragamar mulkin a rajin kansa ga mutumin da ya zaba, shugaba mai ci Miguel Diaz-Canel ya halarci wannan zaman na majalisar.

Labarai masu alaka