Xi Jinping na ziyara a Senegal

Shugaba Xi Jinping na China Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Xi Jinping na China

Shugaban China Xi Jinping ya fara wata muhimmiyar ziyara ta mako guda a Senegal.

A shekarun baya-bayan nan siyasa da tattalin arzikin Senegal na ta bunkasa, shi yasa China ke kallon ta a matsayin wata muhimmiyar kafar shiga kasuwannin Afirka ta yamma.

Dangantaka tsakanin China da Senegal sun habaka cikin sauri, kuma kawo yanzu har an fara samun yabanya. China ta rika mara ma shirye-shiryen gina kasa a Senegal.

A misali, China ta taimaka ma Senegal wajen gina babban dakin ajiye kayan tarihin al'umar bakar fata, da gidan wasannin gargajiya da filin wasan kokawa na kasa.

Ta kuma haka rijiyoyin burtsatse a yankunan karkara, da hanyoyin mota da gadaje da suka bunkasa tattalin arzikin kasar da ke farfadowa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Macky Sall na Senegal

Shugaban Senegal Macky Sall na ganin China za ta taka muhimmiyar rawa a cikin shirinsa na mayar da kasarsa cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki nan da shekara 2035.

Wannan ziyara tana zuwa ne a daidai lokacin da Senegal ke murnar gano tarin arzikin man fetur da gas a karkashin kasa.

Amma kasancewa China ta gina wani makeken yankin kasuwanci a kusa da birnin Dakar, alama ce ta aniyar kasar ta fadada karfin ikonta a yankin Afirka ta yamma ta bangaren kasuwanci da cinikayya.

Amma akwai wadanda basu gamsu da rawar da China ke taka wa a kasar ba. Kuniyoyin kwadado da wasu 'yan kasuwa sun gudanar da zanga-zanga, inda suke nuna rashin amincewarsu da yadda 'yan kasuwar Chinar ke kokarin mamaye bangaren kasuwanci a kasar.

Kazalika, masuntar Senegal na kokawa da yadda jiragen kamun kifi na China ke kamun kifi a tekun kaar babu izinin hukuma.