Faduwar Jarabawa: Makaranta ta kona wayoyin salular dalibai 300

Dalibai a makaranta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dalibai a makaranta

Hukumar wata makarantar sakandare a jihar Arewa ta Ghana ta kwace wayoyin salula dari uku daga hannun dalibai sannan ta kona su.

Hukumar ta kwace wayoyin daga hannun daliban ne a bayan wani rangadin da shugabanni makarantar tare da wasu malamai suka yi a dakunan kwanan daliban.

Malamai a makarantar Damongo Senior High School da ke birnin Accra sun kwace wayoyin dalibai 300, wadanda daga baya hukumar makarantar ta kona su baki daya.

Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis da ta gabata bayan da malaman suka gudanar da wani binciken kwakwaf akan kayan daliban.

An yanke shawarar kwacewa tare da kona wayoyin daliban ne saboda faduwa jarabawa a harshen Ingilishi da daukacin daliban makarantar suka yi a jarabawar WAEC ta bana.

Shugabannin makarantar sun bayyana rashin jin dadinsu game da halayyar daliban. Hukumar makarantar ta ce manufar kwace wayoyin da kona su, shi ne domin daliban su shiga taitayinsu.

Ma'aikatar ilimi ta Ghana reshen jihar Arewa ta goyi bayan hukumar makarantar na daukan wannan matakin.

Amma daliban da abin ya shafa sun koka da matakin da hukumar makarantar ta dauka, kuma sun nemi a gaya masu yadda za su rika tuntubar iyayensu idan bukatar haka ta taso.

Masana harkokin ilimi a Ghana na dora laifin faduwar da dalibai ke yi a harshen Turanci a lokutan jarabawar kammala makaranta ta WAEC akan yawan amfanin da wasu gurbattun kalmomin turanci kamar L.O.L. (Laugh Out Loud) B.R.B. (Be Right Back) da sauransu.

Labarai masu alaka