Mugabe ya juya ma ZANU-PF baya

Robert Mugabe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe

Za a gudanar da zaben shugaban kasa a Zimbabwe, a karon farko tun da aka hambare gwamnatin tsohon shugaban kasar Mista Robert Mugabe.

Mista Mugaben ya shafe shekara 37 yana mulkin kasar, kuma 'yan Zimbabwe sun yi zatan cewa raba shi da mulki zai kawo karshen ikonsa a siyasa, amma batun ba haka ya ke ba.

Masu adawa da mulkin Robert Mugabe na mamakin irin kafewa da karfin zuciya dattijon da ya ke cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa bisa kan karagar mulki.

A zaben da zai gudana a gobe Litinin, Mista Mugabe ya fito karara yana goyon bayan jam'iyyar da ta shafe sheakaru tana kokarin raba shi da mulki, a maimakon jam'iyyar ZANU-PF da ya kafa kuma ya jagoranta har na tsawoon shekara kusan talatin.

Bayan da aka hambare Mugabe daga mulki, abokin tafiyarsa a siyasance, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa, mai shekaru 75 da haihuwa ne ya gaje shi.

Tun da farko Mista Mugabe ya shirya ne matarsa Grace ta gaje shi, amma tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa sun yi mata illa, wanda ya lalata mata duk wata dama da take da ita a siyasance.

Grace Mugabe ce ta yi sanadin korar Mnangagwa daga mukaminsa na mataimakin shugaban kasa, kuma wannan na daga cikin dalilan da suka janyo aka hambare gwamnatin mijinta tare da taimakon sojojin kasar.

Ana kuma zargin ta da hannu a wani harin gurnati da wata kungiya mai suna Genation 40 ta kai kan shugaba Mnangagwa, kungiyar da ita Grace Mugabe ta kafa kuma ta ke jagoranta.

Tun bayan sauka daga mulki da Mista Mugabe yayi, jam'iyyar ZANU-PF ta juya ma Grace Mugabe baya, kuma masu sukarta a ciki da wajen kasar sun lakaba mata sabbin sunaye - suna kiranta 'Disgrace' da 'Gucci Grace'.

Labarai masu alaka