Arsenal na neman Domagoj Vida, Courtois na son komawa Madrid

Dan wasan gaba na Barcelona Ousmane Dembele Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan Barcelona Ousmane Dembele

Yadda ta ke kaya wa a fagen kasuwar 'yan wasan kwallon kafa a Turai, inda ake saye da sayarwan 'yan wasan kwallon kafa dab da bude kakar wasa ta bana.

Wakilin Thibaut Courtois ya nemi Chelsea ta kyale golan dan kasar Belgium mai shekara 26 ya koma Real Madrid inji jaridar Sun.

Liverpool na bukatar dan wasan tsakiya na Wales Aaron Ramsey, mai shekara 27 daga kungiyar Arsenal inji Express.

Da alama dan wasan gaba na Manchester United, Anthony Martial mai shekaru 22 zai yi zamansa a kulob din idan Jose Mourinho bai sami wanda zai maye gurbinsa ba, inji Mirror.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Golan kungiyar Chelsea Thibaut Courtois

An lura dan wasan gaba na Barcelona Ousmane Dembele, mai shekara 21 na tare da 'yan wasan Arsenal kwanan nan, kuma ana hasashen zai iya komawa Gunners, inji Goal.com.

Dan wasan gaba na Chelsea, kuma dan kasar Belgium Michy Batshuayi mai shekara 24 na kan hanyarsa ta komawa Atletico Madrid, inji L'Equipe - ta Faransanci.

Kocin Arsenal Unai Emery na shirya yadda dan wasa baya na Kuroshiya Domagoj Vida mai shekara 29 zaibar Besiktas akan fam miliyan 25 inji Sun.

Dan wasan Monaco kuma dan kasar Aljeriya Rachid Ghezzal mai shekara 26 ya shirya tsaf domin komawa kungiyar Leicester akan fam miliyan 12.5 inji L'Equipe - ta Farnsanci.

Labarai masu alaka