Daliban arewacin Najeriya sun yi bajinta a Afirka

Daga dama: Peter Balarabe, Fatima Auwal Aliyu, da Salisu Yusuf Bako

Asalin hoton, Muhammad Ibrahim Jega

Bayanan hoto,

Daliban uku dai sun fito ne daga Jihar Kaduna ta arewacin Najeriya

Daya na karatu ne a Jami'ar Abuja; biyu kuma a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Amma daliban uku—Fatima Auwal Aliyu, da Peter Balarabe, da Salisu Yusuf Bako—sun yi tarayya a wasu abubuwa: dukkansu 'yan arewacin Najeriya ne, kuma Kimiyyar Kwamfiyuta (Computer Sceince a Turance) suke karantawa a jami'a, kuma dukkansu suka hadu suka kirkiri wata manhajar wayar salula.

"Mutum zai iya amfani da wannan manhaja a wayarsa ta salula ya kunna abubuwan da ke cikin gidansa, kamar su fanka, kamar su talabijin, kamar su soket haka.

"Mutum daga wayarshi a hannunsa zai iya kunna wadannan abubuwa", in ji Fatima.

Wannan manhaja dai za ta yi aiki ne a kan waya komai-da-ruwanka mai amfani da tsarin Android ko iOS.

A cewar Salisu, "Idan muka sa maka ita a wayar salularka, sannan akwai na'ura da muka hada wadda za mu saka maka a gida. To da wannan manhajar [da na'urar] ne za ka rika kunnawa da kashe duk kayan da kake so."

Bayanan hoto,

Za a iya amfani da manhajar a wayar salula a kashe ko a kunna fitilun lantarki ko fanka ko talabijin

Hikimar kirkirar wannan manhaja dai, inji Peter, ita ce: "mun yi tunani ne na yadda za mu saukaka wa 'yan Afirka—musamman 'yan Najeriya—rayuwa."

Su biyu ne dai suka fara wannan tunani, kafin Fatima ta shigo cikinsu a yi tafiyar da ita, tun da a cewarta, "in dai har ra'ayoyin mutane suka zo daya, haduwa a yi irin wadannan abubuwa ba ta wahala".

Kafin zuwan na Fatima, jami'an kungiyar Startup Arewa mai karfafa wa matasan arewa gwiwa sun rungumi harkar fasahar kirkire-kirkire ne suka fara tuntubar su.

Ko da yake shida daga cikin kasashe 10 da aka yi amannar tattalin arzikinsu na bunkasa cikin hanzari a duniya a Afirka suke, nahiyar ce koma-baya ta fuskar bunkasar harkar kula da lafiya da kula da bukatun nakasassu.

Don haka ne wata gasa da aka saba gudanarwa duk shekara a kan kirkirar butunbutumi (wato robot a Turance), Pan African Robotics Competition, ta kalubalanci daliban nahiyar su kirkiri fasahohin da za su taimaka wajen inganta harkar kula da lafiya da rayuwar nakasassu.

Ko da jami'an Startup Arewa suka rungumo wannan kalubale suka ce wa Salisu da Peter "kule!", daliban ba su bata lokaci ba suka ce "cas!"

"Da labarin wannan gasa ya zo mana, sai suka ce suna so ne mu kirkiri wata na'ura da za ta saukaka rayuwar mutanen da ke fama da matsalar gani ko wadanda ba sa iya tafiya. Da ma muna tunanin yin wani abu irin haka, to sai muka ga ga dama ta samu", inji Salisu.

Asalin hoton, Muhammad Ibrahim Jega

Bayanan hoto,

Daliban na aiki da kungiyar Startup Arewa don ganin wannan manhaja tasu ta yadu

Sai dai wani hanzari ba gudu ba: a cewar shugaban kungiyar ta Startup Arewa, Mohammed Ibrahim Jega, akwai bukatar a samu mutum na uku da zai shigo a yi tafiyar da shi, kuma kamata ya yi a samu mace.

Don haka aka tuntubi Fatima—wadda da ma tana sha'awar yin wani abu don inganta harkar kiwon lafiya don kuwa tuni ta fara aikin samar da wani shafin intanet don ya taimaka wa mahaifiyarta wacce ma'aikaciyar lafiya ce—ta kuma amsa.

Daga karshe dai daliban sun shiga jerin wasu kungiyoyin dalibai wadanda suka hadu suka wakilci Najeriya a gasar wadda aka gudanar a Senegal a karshen watan Yuli.

Wannan manhaja da wadannan dalibai suka kirkiro ce dai ta zo ta hudu a karshen gasar—kuma yanzu haka suna aiki tare da kungiyar Startup Arewa don ganin an samu masu zuba jari an yawaita na'urar da manhajar saboda mutane su amfana.