Ghana ta sallami ministan makamashi daga bakin aiki

Nana Akufo Addo
Bayanan hoto,

Tun a lokacin yakin neman zabe, jam'iyya mai mulki ta sha alwashin gudanar da bincike

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ya sallami ministan makamashin kasar daga bakin aiki.

Wani bayani daga fadar shugaban kasa ya kara da cewa an umarce shi da ya mika mukamin sa hannun ministan filaye da ma`adinan kasa wanda zai yi rikon kwarya kafin a nada sabon ministan.

Sallamar ministan makamashin Mista Boakye Agyarko ta fara aiki nan take ne bayan fitowar wata 'yar gajeriyar sanarwa, dauke da rattaba hannun daraktan sadarwa na fadar shugaban kasa Mr Eugene Arhin.

Duk da yake babu wani dalili da aka bayar na sallamar ministan daga aiki, amma masu sharhi na zargin hakan ba ya rasa nasaba da yarjejeniyar makamashi ta Ameri, wadda aka shiga tun lokacin tsohowar gwamnatin NDC, wadda kuma jam`iyya mai mulki ta NPP ta yi ta suka tare da shan alwashin soke ta da zarar ta hau mulki.

Ministan makamashin ya fara shan matsin lamba ne tun bayan da ya yi ikirarin yunkurin sake sabunta yarjejeniyar ta Ameri, kan hujjar cewa ta fi wacce aka kulla a baya.

Sai dai wasu manyan jami`an hukumar samar da makamashi Volta River Authority sun gardamar cewa, ikirarin da ministam ya yi na kebe wa Ghana dala miliyan hudu saboda sabunta yarjejeniyar ba shi da tushe bare makama.

A cewar su, idan majalisar dokoki ta amince da yarjejeniyar za ta iya janyowa kasa asarar kudi dala milyan 472

Yayin da wata wasikar da ake zargin ta fito ne daga kamfanin Ameri ta mamaye shafukan sada zaumunta, da ta musanta cewa kamfanin ya san da maganar sake sabunta yarjejeniyar Ameri da aka rattabawa hannu 2015 lokacin tsohuwar gwamnatin NDC.