WHO: Rashin motsa jiki barazana ne ga lafiyar al'umma

Motsa jiki na da matukar muhimmanci
Bayanan hoto,

Rahoton ya ce teba na janyo ciwon zuciya

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa kusan kwatar al'ummar duniya ne ke cikin hadarin kamuwa da manyan cututtuka, saboda rashin motsa jiki.

An dai wallafa rahoton da WHO ta fitar a mujallar kiwon lafiya ta Lancet global Health bayan tattaunawa da kusan mutum miliyan biyu.

An gano kalilan daga cikin matasa ne ke da karsashi a lokcin da aka yi binciken tsakanin shekarun 2001 da 2016.

Haka kuma WHO ta ce mutanen da ba sa motsa jiki kwata-kwata na cikin hadarin kamuwa da ciwon zuciya, da ciwon siga da cutar Kansa.

Wani abin tashin hankali game da binciken da aka gudanar, an gano cewa sama da matasa biliyan daya nn cikin hadarin kamuwa da cutattuka masu alaka da toshewar magudanar jini inda farat daya zuciyar mutum ka iya bugawa saboda rashin motsa jiki.

Sama da kashi 40 cikin 100 na Amirkawa ragwaye ne, yayin da lamarin ya kazanta a wasu kasashe ciki har da gabas ta tsakiya, inda rahoton ya ce matsalar ta fi kamari a kasashen Iraqi da Saudiyya.

Binciken ya ce mace daya cikin uku da kuma namiji daya cikin hudu ba su motsa jikinsu yadda ya kamata na akalla minti 150 a mako.

Sannan rabin mutanen da suka kai shekarun girma ba sa tabuka abin azo a gani kamar yadda ya kamata domin kare lafiyarsu ciki har da rashin motsa jiki.

Rahoton ya yi kira ga kasashe su karfafawa mutane gwiwar motsa jiki ta hanyar samar da abubuwan da za su sa mutane yin tafiya da kuma wuraren wasanni.

Likitoci sun bada shawarar cewa ya kamata a kowacce rana 'yan Adam su dinga matsakaicin motsa jiki, misalin tafiyar kasa ko sassarfa da sauransu.