Guguwar Jebi na ci gaba da daidaita Japan

Birnin Kansai ya fi lalacewa
Bayanan hoto,

Gine-ginen gwamnati da ayyukan more rayuwa sun daidaice

A kasar Japan an yi amfani da kwale-kwale masu gudun gaske dan kubutar da dubban fasinjojin da mahaukaciyar guguwar nan da ta afkawa kasar ta rutsa da su a filin tashin jiragen sama.

guguwar da Japan bata taba gani ba cikin shekaru 25, ta janyo mummunan yanayi a filin jirgin sama na Kansai da ke kudancin tsuburin Bay da ke gabashin kasar.

Hotunan tauraron dan adam sun nuna lokacin da kakkarfar iska ta hankado wata tankar mai gefen gada, ya yin da kanana da manyan motoci sun yi ta karo da juna da yin tsalle kamar an jefasu zuwa dayan bangaren.

A yankin Nishinomiya da ke gabatar teku kuwa kusan motoci 100 ne da aka shigo da su ta jirgin ruwa aka kasa fito da su sakamakon katsewar wutar lantarki.

Guguwar mai suna Jebi ta hallaka mutane 9, ya yin da daruruwa suka ji munanan raunuka.

Sama da miliyan daya kuma suka rasa muhallansu musamman a birnin Osaka, babu wutar lantarki sannan hanyoyin sun lalace hakan na janyo tsaikon aikin ceto.

Guguwar Jebi na zuwa ne mako guda bayn wata mahaukaciyar guguwar ta Cimaron ta daidaita kudancin yankin Kansai.

Tun da fari guguwar ta fara yada zango ne a tsuburin Shikoku da ke kudu maso gabashin Japan, sannan ta nausa gundumar Kobe On Honshu.