An samu karin reshen kungiyar al-Qae'da a Mali

Osama bin Laden

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana kallon Osama bin Laden a matsyin kashin bayan kirkiro kungiyar al-Qaeda

Amirka ta sanya sunan wata kungiya a jerin ta 'yan ta'adda, bayan ta kira kan ta reshen al-Qa'eda a kasar Mali.

Gamayyar kungiyoyi uku masu dauke d makamai su ne suka samar da kungiyar Jama'atu Nusrat al-Islam wal-Muslimin, ta kuma yi ikirarin kai hare-haren da akai asarar rayuka a kasar a watan Mayun bara.

Ayyana ta a jerin 'yan ta'adda na nufin Amirka za ta dauki mataki kan ta kamar sauran kungiyoyin 'yan ta'adda irin IS.

Sannan haramcin mu'amala da ita ya rataya a wuyan duk Amirkawa kam daga musayar kudade da sauransu.