Ana caccakar Trump a fadarsa

Mista Trump ya kira jaridar New York Times da makaryaciya
Shugaba Donald Trump na Amurka, ya bukaci jaridar New York Times ta bayyana cikin jami'ansa wanda ya rubuta sharhi a jaridar kan cewa suna aiki tukuru da bin hanyoyi na kare kasar daga munanan muradunsa.
Wanda ya yi rubutun dai ya yaba wa wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin ta samu, inda ya ce sun samu ne ba don matakan da mista Trump ke dauka a tsarin shugabancinsa ba.
Mista Trump ya danganta bayanan da abin kunya tare da kiran jaridar ta jabu kuma makaryaciya bayan wallafa labarin da ya kira mara tushe.
Jaridar dai ta boye sunan marubucin.
Wannan kuma ya kara rura wutar rikici a fadar White House inda tuni wutar ke ci bayan littafin da tsohon dan jarida Bob Woodward ya rubuta game da gwamnatin Trump da jaridar Washington post ta wallafa kuma za a fitar ranar talata.
Jaridar The Times kuma ta kare bayanan da ta wallafa, inda kakakin jaridar ya ce suna alfahari da suka wallafa, domin zai yi matukar tasiri ga jama'a wajen fahimtar abin da ke faruwa a gwamnatin Trump.
Marubucin ko marubuciyar da aka sakaya suna ya kuma nuna gamsuwa da nasarorin da gwamnatin ta samu, amma kuma ya ce an samu cimma nasarorin ne ba don saboda Trump ba.
Asalin hoton, Getty Images
A cikin wata sanarwa, kakakin fadar White House ta ce wanda ya yi ko ta yi rubutun ya nuna ba kishin kasa ba ne ya sa ko ta sa a gaba.