An kashe mayakan Houthi 70 a rikicin Yemen

Asalin hoton, AFP
Ma'aikatan jinya a yankin Hudaida sun ce mayakan Houthi 70 ne aka kashe a sabon fadan da ya barke, kuma sojojin gwamnatin 11 ma sun rasa rayukansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi ta kokarin sasanta tsakanin bangarorin biyu a wani taro da ta shirya a Geneva babban birnin Switzerland a makon jiya.
Amma 'yan tawayen sun ki halartar taron, wanda ya janyo tilas aka dage shi.
A yanzu babbar damuwa ita ce fada na iya bazuwa zuwa wau sassan kasar saboda rashin wani tsari na sulhu.
Masu aikin agaji a kasar na ganin cewa yunkurin kwace tashar jirgin ruwa ta hudaida daga hannun mayakan Houthi na iya dakatar da shigar da kayayakin agaji da 'yan kasar ta Yemen ke bukata matuka.