'Yara kusan rabin miliyan za su mutu a bana'

Save the Children ta ce yunwa na galabaitar da yara a yankunan da ake yaki Hakkin mallakar hoto SAVE THE CHILDREN
Image caption Save the Children ta ce yunwa na galabaitar da yara a yankunan da ake yaki

Kungiyar agaji ta Save the Children ta kiyasta cewa yara sama da rabin miliyan da shekarunsu ba su haura biyar ba, za su mutu a wannan shekarar saboda tsananin yunwa a kasashe da yaki ya kassara.

Kungiyar ta ce bangarorin da ke rikici da juna na datse hanyoyin bada taimakon agaji da gangan.

Save the Children, ta ce alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa akwai yara sama a 1400 da suka fada cikin wannan yanayin a bara, bayan hana shigar da kayayakin jin-kai yankunan da ake rikici.

Karuwar alkaluman a cewar kungiyar ya biyo bayan rikicin Sudan ta Kudu da Yemen da Mali da kuma Syria.

Shugaban kungiyar Kevin Watkins ya ce amfani da yunwa a matsayin makamin yaki na neman zama ruwan dare.