Kamfanin Apple ya gargadi Amurka kan takunkumin China

Wayar Apple mai suna iPhone Hakkin mallakar hoto Getty Images

A yau Laraba ne aka sa ran cewa kamfanin Apple zai fito da wasu sabbin na'urori a wajen wani kasaitaccen biki da zai gudana a shalkwatar kamfanin da ke Cupertino a jihar California ta Amurka.

Wannan bikin na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ke nuna damuwarsa dangane da matakan da shugaban Amurka Donald Trump ke shirin dauka na gindaya wa kasar China wasu sabbin takunkumai na ciniki.

Wannan ne biki na farko da kamfanin Apple ya shirya tun da ya zama mai karfin jarin da ya zarce dala trilliyan daya.

Amma babu wasu sababbin na'urorin da kamfanin zai samar, domin tuni aka tsegunta wa jama'a cewa kamfanin zai samar da wayar nan ta iPhone mai farin jin amma wadda ta fi ta da girma.

Ana kuma sa ran Apple zai sabunta agogon hannu na Apple Watch wanda zai rika duba bugun zuciyar wanda ke sanye da agogon.

Wasu kuma na ganin kamfanin zai fitar da wata komfuta mai saukin kudi a karon farko - domin dalibai.

Babu wanda ya tabbatar da ko nawa kamfanin zai rika sayar da wadannan sababbin na'urorin.

A makon da ya gabata ne kamfanin ya rubuta wata wasika zuwa ga shugaban Amurka DT, inda yayi gargadin cewa sanya wa kasar China wasu sabbin jerin takunkumai zai sa na'urorin kamfanin su kara tsada ne kawai.

Amma shugaban na Amurka ya mayar wa da kamfanin martani, inda ya ce kayan kamfanin za su rage tsada idan ya rika kera na'urorinsa a gida Amurka maimakon zuwa China.