Jirgin ruwa ya yi hadari a Tanzania

Tanzania
Image caption Masu aikin ceto sun kubutar da kusan mutane 100, cikinsu sama da mutum 30 su na cikin mawuyacin hali

Wani jirgin ruwa makare da daruruwan mutane ya yi karo a tafkin Vicoria da ke kasar Tanzania, inda mutane 40 suka mutu.

Wani jami'in gwamnati ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ce wa adadin wadanda suka nutse ka iya kai wa 200, babbar damuwar da ake da ita shi ne an dakatar da aikin ceto har zuwa yau juma'a.

Jirgin mai suna NV Nyerere ya sha kwana ne a cikin tafkin kusa da tsuburin Ukoro da Bugolora.

Hukumomi sun yi zargin jirgin an makare shi da mutane sama da 400, dalilin da ya kife kenan a lokacin da ya ke sha kwana mutanen suka koma bangare guda kuma nan take ya tunzura.

An yi nasarar ceto kusan mutane 100, kuma 32 daga cikinsu su na cikin mawuyacin hali kwance a asibiti.

Cikin wadanda suka mutu har da ma'aikacin da ya ke bata tikitin shiga jirgin ruwan, dan haka na'urar da ke adana bayanan wadanda suka sayi tikiti ta bata kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Tanzania dai ta sha fama da bala'o'i daban-daban da suka shafi tuntsurewar jiragen ruwa sakamakon cika shi da fasinjoji ba bisa ka'ida ba.

A shekarar 1999 jirgin ruwa samfurin MV Bukoba ya yi hadari a tafkin Victoria, shi ne hadari mafi muni da kasar ta gani a tsakanin shekarun inda mutane 800 suka mutu nan take.

Sai kuma shekarar 2011 kusan mutane 200 ne suka mutu a Zanzibar sakamakon nutsewar da jirgin ruwa makare da mutane ya yi.

Haka ma a shekarar 2012 mutane 145 ne suka mutu a lokacin da jirginsu ya yi karo a tsuburin Zanzibar.

Labarai masu alaka