Ma'aikata sun maka Unilever a kotu

Unilever ya ce ya na bai wa ma'aikatansa duk wani taimako da suke bukata Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Unilever ya ce ya na bai wa ma'aikatansa duk wani taimako da suke bukata

Wasu ma'aikata su 10 a Kenya sun shigar da karar kamfanin Unilever na Burtaniya da Holland a gaban kotun koli da ke London, akan gaza daukan nauyin da ya rataya a wuyansa na kare hakkin dan adam a rikicin bayan zaben shekara ta 2007.

Ma'aikatan sun ce kamfanin ya nuna halin ko-in-kulla wajen kare rayukansu a lokacin, zargin da Unilever ya musanta.

Sama da mutum dubu 1 aka kashe a rikicin.

A lokacin shigar da karar ma'aikatan sun ce akwai masu yiwa kamfanin aiki su 7 cikin wadanda aka kashe, sannan an aikata fyade akan mata 56.

Wakilin BBC ya ce ma'aikatan sun ce shugabanin gudanarwar kamfanin a Kenya sun jefa rayuwarsu a cikin hatsarin barazanar mutuwar bayan ma'aikatan sun shigar da korafinsu.

Sai dai Unilever ya ce ya bai wa ma'aikatansa duk wani taimako da suke bukata a wannan lokaci.

Labarai masu alaka