Masu cutar AIDS sun karu a China

Cutar HIV na karuwa a China Hakkin mallakar hoto Science Photo Library

Kasar China ta sanar da cewa an samu karuwar 'yan kasar da suka kamu da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV ko kuma AIDS da kaso 14 cikin 100 a cikin shekara guda.

Hakan ya kai adadin masu dauke da cutar fiye da dubu 820.

Jami'an lafiya a kasar sun ce a cikin zangon shekara na biyu kadai, an samu mutane fiye da dubu 40 da suka kamu da cutar.

Mahukunta a kasar sun ce yawanci wadanda suka kamu da cutar sun kamu da ita ne ta hanyar jima'i ba kamar a baya ba, inda ake samun yaduwarta ta hanyar karin jini.

Wannan dalili ya sa gwamnatin kasar nuna damuwa kwarai da gaske tare da fara neman mafita a kan yaduwar cutar ko kuma karin masu kamuwa da ita.

Tun a shekarar 2003, gwamnatin kasar ta China ta yi alkawarin samar da magungunan cutar HIV , a wani yunkuri na magance matsalar yaduwarta.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka