An kammala zabe a jamhuriyar Kamaru

Poul Biya
Image caption Shugaba Poul Biya ya kai shekaru 36 kan karagar mulki

An kammala kada kuri'a a zaben da aka yi a Jamhuriyar Kamaru, wanda shugaba Poul Biya da ya fi kowa dadewa kan karagar mulki a nahiyar Afirka na tsawon shekaru 36 ya sake tsayawa takara.

Ana sa ran za a dauki kwanaki kafin a kammala kidayar kuri'un, an kuma samu rahotannin tashin hankali da ya barke a yankin 'yan a ware masu amfani da turancin Ingilishi.

An ji karar harbe-harbe, yayin da aka aike karin jami'an tsaro don tabbatar da oda a Bamenda Buea.

Daya daga cikin masu sanya ido kan zaben Adamou Ibrahim, ya shaidawa BBC cewa zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Kuma ya ce mutane sun fito domin kada kuri'a.

Sai dai akwai 'yan takara biyu da suka sanar da hade wa a kurarren lokaci.

Ibrahim ya ce kasa da sa'o'i 48 a gudanar da zaben jam'iyyun suka sanar da hukumar zabe hadewarsu.

Hakan ya janyo an samu dan rudani saboda babu isasshen lokacin buga wata kuri'ar, amma duk da haka za su yi amfani da dabarar duk kuri'ar da aka gani an zabi daya daga cikin hadakar jam'iyyun, za a kidaya ta karkashin daya daga cikinsu, idan an zo tattara sakamako.

Labarai masu alaka