Zaftarewar kasa ta kashe sama da mutum 30 a Uganda

Zaftarewar kasa a Uganda Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ambaliyar ruwan ta kwashe gidaje da dama a yankin

Akalla gawarwaki 30 ne aka gano bayan da mamakon ruwan sama ya janyo zaftarewar kasa a gabashin Uganda ranar Alhamis.

Jaridar kasar ta New Vision ta ruwaito cewar ana zaton daruruwan mutane sun mutu bayan da wani rafi ya yi ambaliya, inda ruwan ya cinye kauyuka da wata kasuwa a yankin Bududa da ke gabashin Uganda.

Jaridar ta bayyana cewa shugaban yankin Bududa, Wilson Watira ya ce kawo yanzu gawarwaki 40 ne a ka gano ba 31 ba kamar yadda AFP ya ruwaito.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane sama da talatin ne a ke zaton sun mutu dalilin zaftarewar kasar

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ce an tura tawagar masu bayar da agaji yankin, kuma gwamnati za ta duba hanyoyin da za a bi domin kare afkuwar irin wadannan bala'o'in.

"Ina mika sakon ta'aziyyata ga wadanda su ka rasa 'yan uwansu a wannan mummunan bala'i," ya ce.

A na ganin cewa yawan mutanen da su ka mutu zai karu a yankin Mount Elgon.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yankin Baduda na da yalwar kasar noma wanda ke sa daruruwan mutane zama a yankin

Wannan dai ba shi ne karo na farko da zaftarewar kasa ta faru a yankin Baduda ba.

A 2010, mutane sama da 300 ne su ka mutu bayan wata zaftarewar kasa mai muni a yankin, kuma an bukaci al'ummomin da ke zaune a wajen da su tashi.

Sai dai ba su saurari gargadin ba, don kuwa sun koma yankin kuma sun ci gaba da noma kamar yadda su ka saba.

Yankin Baduda na da yalwar kasar noma, don haka ya ke da tarin jama'a.

Labarai masu alaka