Jirgin sama ya fadi da fasinjoji sama da 180

A shekara ta 2013 jirgin na Lion Air ya fada a teku sai dai dukkanin fasinjojinsa sun tsira da rayukansu

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A shekara ta 2013 jirgin na Lion Air ya fada a teku sai dai dukkanin fasinjojinsa sun tsira da rayukansu

Wani jirgin saman fasinjar Lion Air ya yi hadari a teku Java jim kadan bayan tashinsa daga birnin Jakarta na Indonesia.

Fasinjoji fiye da 180 ke cikin jirgin Kirar Boeing 737, wanda ke kan hanyar zuwa yankin Pangkal Pinang da ke tsibirin Bangka.

Tuni aka tura tawagar masu bincike da aikin ceto yankin, sai dai babu tabbacin ko an samu wadanda suka rage da sauran rai a jirgin.

Jami'ai da ke aiki a kamfanin man kasar ta Indonesia sun ce sun ga tarkacan jirgin, ciki harda kujerun fasinjoji a cikin ruwa da ke kusa da inda suke aiki a teku.

Shugaban kamfanin jirgin ya bayyana cewa a yanzu ba za su iya cewa komai ba a game da hadarin, inda ya ce suna kokarin tattara bayanai ne.

Jirgin dai ya fara aiki ne a 2016, sannan kuma ya zamo mallakin Lion Air a watan Augustan da ya wuce.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan uwan fasinjojin jirgin sun shiga alhini a Jakarta

Wani jami'i a hukumar sufuri ta kasar ya shaida wa BBC cewa dama jirgin yana da 'yan matsalolinsa tun da aka kawo shi kamfanin.

Yawanci al'ummar kasar ta Indonesia sun raja'a ne a kan tafiye-tafiye a jirgin sama, amma kuma mafi akasarin jiragensu na da 'yan matsaloli nan da can.

Indonesia na cikin kasashen da ke fuskantar koma baya a harkokin sufurin jiragen sama, ko a shekarun baya-baya nan ta fuskanci irin wadanan hadura.