Fitacciyar 'yar jaridar Nijar ta rasu

Shugaba Muhammadu Issoufou na Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Issoufou na Nijar ya nuna alhinisa da mutuwar marigayiya Mariama

A jumhuriyar Nijar an rawaito cewa mace ta farko 'yar jarida a kasar Mariama Keita ta rasu a jiya litinin.

Mariama Keita ta rasu ta na da shekara 72, bayan ta yi fama da jinya kamar yadda 'yan uwanta su ka sanarwa kafofin watsa labarai na kasar.

An dai haifi Mariama Keita ne a shekara ta 1946 a birnin Yamai, ta kuma rike mukamin darakta a babban gidan Rediyon kasar mallakar gwamnati wato muryar sahel ko voix du sahel.

Madam Keita ta shugabanci hukumar sadarwa ta kasar Nijar wato CSC daga shekara ta 2003 zuwa 2006.

Ta kuma jagoranci wata kungiya ta hadaka ta mata da ta kunshi kungiyoyin mata kusan 50, da suka halarci taron wayar da kai game da abun da kudin tsarin mulkin kasar ya kunsa a shekara ta 1993.

Tuni dai aka shiga alhinin wannan rashi da aka yi a kasar.