Yadda za a sasanta tsakanin gwamnati da 'yan Shi'a

  • Sani Aliyu
  • Multimedia Broadcast Journalist
Members of Islamic Movement of Nigeria (IMN) wave flags and chant slogans as they take part in a demonstration to protest against an imprisoned Shiite cleric, in Abuja

Asalin hoton, Getty Images

Rikici tsakanin mabiya Shi'a da jami'an tsaron Najeriya ya dauki wani salo mai ban tsoro, inda duk lokacin da suka yi artabu, sai ka ji an kashe ko raunata wasu daga cikinsu.

A watan Disambar 2015 wani rikici da ya hada da mabiya babban malamin Shi'a a Najeriya, Mallam Ibrahim El Zakzaky, da wani ayarin sojojin kasar da ke rakiyar babban hafsan sojojin kasar ya janyo zubar da jini.

Bayan da kura ta lafa, kungiyar Shi'a ta ce sojojin sun hallaka daruruwan mabiyanta wadanda daga baya aka binne su gaba daya a cikin wasu manyan kaburbura.

Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenah Ibrahim sun sami raunuka a sanadiyyar harbin da sojoji su kayi masu, kuma hukumomin kasar suna tsare su a wani kebabben wuri na kusan shekara uku.

Matakan da sojojin Najeriya ke dauka kan kungiyar 'yan Shi'an ya taso da wasu tambayoyi game da iya tafiyar da wannan kalubalen a bangaren sojojin Najeriya.

Masana na ganin cewa ci gaba da tsare Ibrahim Zakzaky tare da matarsa, duk da cewa kotu ta bayar da umarnin a sake su ya iza wutar kiyayya ga hukumomi a bangaren al'ummar Shi'a a kasar.

Masana na gani cewa nan ba da jimawa ba ana iya fuskantar wata gagarumar matsalar tsaro musamman idan aka duba yadda kungiyar Boko Haram ta yi karfi saboda hukumomi sun yi amfani da karfin soji wajen yunkurin murkushe kungiyar.

Kisa da aka yi wa shugaban kungiyar Boko Haram Muhammed Yusuf da daruruwan mabiyansa a shekarar 2009 ya ruruta rikicin inda ya ba wani bangare na kungiyar ya kwace ragamar tafiyar da ita.

Asalin hoton, Getty Images

Sharhin Kabiru Adamu

Kabiru Adamu, wani mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya ne, ya bayyana wa BBC damuwarsa kan yadda hukumomi da 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi ke kara tayar da hankulan al'ummar kasar.

"Matsala ce wadda kusan za a iya kauce ma ta, dalili kuwa shi ne an shafe shekaru matsalar ta ki ci ta ki cinyewa."

Ya kara da cewa, "Kuma aka zo aka kama shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi, sannan ita kungiyar ta nace sai ta cigaba da yin mazaharar da take yi. Kuma abin da ke tayar da hankali, da a Zaria su ke in mazaharar, amma ga shi yanzu matsalar ta bazu zuwa Abuja."

Ya ce dukkan bangarorin sun ja daga, kuma da alama doka ba ta yi aiki ba kenan.

"Matakan da hukumomin Najeriya ke dauka na iya mayar da wannan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi ta rikide ta koma ta ta'addanci," a cewar masanin.

Asalin hoton, Getty Images

Bata suna da martabar Najeriya a idon duniya - Bulama Bukarti

Barista Abdu Bulama Bukarti, wani mai nazari a Gidauniyar Tony Blair da ke birnin Landan ya ce zubar da jinin dan adam mummunar al'amari ne, ba a wurin mahaliccinmu ba kawai, har ma a karkashin dokokin Najeriya da na kasa-da-kasa."

Ya kara da cewa kotun da ke hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, ICC, na bibiyar halin da jami'an tsaron Najeriya da mabiya Shi'a suka sami kansu a game da wannan lamarin.

"Wannan lamari na bata suna da martabar Najeriya a wurin kasashen duniya, kuma nan gaba ana iya shigar da kara a gaban wannan kotu domin daukan mataki akan jami'an tsaro da hukumomin Najeriya."

Shin laifin na wane ne?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Masu lura da yadda 'yan Shi'a ke gudanar da mazahara ta shekara zuwa shekara sun dora laifi a kan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Najeriya a bangare daya:

"A sauran kasashen duniya, duk lokacin da 'yan Shi'a suka fita zuwa tattaki, su kan bi tsarin doka da oda na kasar, da kuma bisa sanin ya kamata da dacewa", in ji Bulama Bukarti.

Ya kara da cewa "Amma a Najeriya sai ka ga akasin haka lamarin ya ke.

"Duk lokacin da mutane suka fita zuwa sabgoginsu, sai ka taras da mabiya Shi'a sun tare hanyoyi, kuma sun take wa sauran al'umma hakkokinsu na walwala da 'yancin zuwa wurin da suke so."

A bangaren jami'an tsaro kuwa, ya ce, "Kowane jami'in tsaro ya san cewa idan ya raunata dan kasa ko ya kashe shi, ya san doka za ta iya yin aiki a kansa."

Ya bayyana cewa a Najeriya ba haka lamarin ya ke ba, inda ya bayar da misalin adadin alkaluman da kwamitin binciken rikicin jami'an tsaro da 'yan Shi'a na Zaria a 2015.

"A wannan shekarar, fiye da mutum 300 kwamitin bincike ya gano cewa sojoji sun kashe, kuma kwamitin ya umarci a hukunta sojojin da suka aikata laifin, amma har yau ba mu ji wanda aka kai kotu ba."

Mafitar Shari'a

Kabiru Adamu ya bayar da wasu shawarwari. Ya bayyana cewa dukkan hanyoyin da za a bi na samo maslaha suna karkashin abin da bature kan kira "exit strategy", wato mafita.

"Da farko ya kamata a bi tsarin shari'a. Ko dai gwamnati ta bi umarnin kotu da ke cewa a saki shugaban kungiyar, ko kuma ta daukaka kara zuwa wata kotun, domin gamsar da kotun dalilanta na ci gaba da rike shi."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu 'yan kasar da dama na ganin Shugaba Buhari ba ya abin a zo a gani kan sasanta rikicin shi'a

Ya bayar da shawarar cewa ya kamata dukkan bangarorin biyu su kai zuciya nesa, kuma a sami wata tattaunawa tsakaninsu domin a sa wadannan 'yan kungiyar ta Shi'a su rika bin dokoki, kuma su rika girmama jami'an tsaro".

Sharhin Bashir Mijinyawa

Wani mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Najeriya, Bashir Mijinyawa ya ce:

"Sarkin Musulmi da kungiyar MURIC mai rajin kare hakkin Musulmi a Najeriya sun tsame hannayensu daga rikicin 'yan Shi'a da hukumomin kasar."

"Ina ganin rikicin ya kai wani matakin da yake bukatar sulhu na gaggawa."

"Ina kuma ganin cewa dukkan bangarorin biyu na da laifi wajen ruruta wutar rikicin."

"Abu na farko da 'yan Shi'a ya kamata su gane shi ne ba su da goyon bayan Musulmin kasar baki daya saboda halayyarsu ta muzgunawa sauran al'umomin kasar a duk lokacin da suka fita yin tattaki."

"Abu mafi muhimmanci shi ne babu wata kungiya ko al'umma da ke da ikon mamaye hanyoyin da aka samar domin kowa wajen biyan bukatarsu su kadai."

"Wannan halayyar ce ke kai ga take hakkokin sauran 'yan kasa da suke kokarin biyan bukatunsu na yau da kullum."

"Kuma ya kamata 'yan Shi'a su gane cewa babu wata gwamnati a duniya da za ta kyale wata kungiya ko mutane su take hakkin sauran al'umomin kasar."

"A daya bangaren kuma, a fili take cewa gwamnatocin Najeriya ba su nuna kwarewa da dattakun da ya kamace su ba wajen samar da mafita ga wannan matsalar ta 'yan Shi'a."

"Kowa ya san cewa wata babbar kotu ta umarci gwamnati ta saki Ibrahim El Zakzaky, shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi, har ma ta ce a biya shi Naira miliyan 50 saboda tsare shin da aka yi babu shari'a."

"Amma gwamnatin ta yi kememe, ta ki bin umarnin kotun, saboda wai 'tana rike da shi ne domin kare lafiyarsa'."

"Yawancin masana harkar shari'a a Najeriya na ganin cewa gwamnatin ta yi sakaci wajen gudanar da shari'arta da Ibrahim El-Zakzaky."

"Suna ganin da an hanzarta kammala shari'ar, da tuni matsalar ta wuce, ko da ko daure shi aka yi."

"Matsalar mai tayar da hankali a yau ita ce ta yadda ake asarar rayukan mabiya Shi'a a duk lokacin da suka yi arangama da jami'an tsaro, lamarin da yanzu ya kai shekara uku babu mafita."

"Akan haka nake kira ga Sarkin Musulmi, wanda shi ne shugaban Musulmin Najeriya da ya shiga tsakani domin sasanta gwamnati da 'yan Shi'a."

"Ina kuma kira ga sauran manyan malamai da masu fada aji a ciki da wajen kasar, da su taimaka wa Sarkin Musulmi wajen sauke wannan nauyin, domin samar da mafita ta siyasa ga wannan matsala da ta ki ci ta ki cinyewa."

Asalin rikicin 'yan Shi'a da hukumomin Najeriya

Wannan rikicin ya fara ne tun gabanin zuwan gwamnatin Muhammadu Buhari a 2015.

Ana iya cewa a watan Satumba 1996 zuwa watan Maris na 1997, babban rikici na farko ya auku tsakanin hukumomin Najeriya karkashin gwamnatin mulkin soja ta Janar Sani Abacha.

A wancan lokacin sojoji sun yi wani artabu da 'yan sanda a birnin Zaria da ke arewacin kasar, inda jami'an 'yan sanda suka kashe wasu daga cikin mabiya Shi'a da suka fita bisa titunan birnin domin neman a saki malaminsu, Ibrahim Zakzaky.

Karin labaran da za ku so ku karanta: