China ta dage haramcin cinikin karkanda

Karkanda
Bayanan hoto,

Ana amfani da hauren karkanda da kashin damisa wajen yin magungunan gargajiya a kasar China

Gwamnatin China ta dage haramcin kasuwancin kashin Damisa da hauren karkanda, da aka sanya sama da shekaru 25.

Sai dai matakin ya harzuka masu rajin kare hakkin dabbobi, wadanda ke ganin hakan zai kawo cikas kan kokarin da kasashen duniya ke yi na kare dabbobin daga barazanar masu fataucin hauren ba bisa ka'ada ba.

Ana amfani da kashin damisa da hauren karkanda dan yin magungunan gargajiya kasar ta China.

Amma ba kowanne asibiti ne a China ta amince likitoci su yi amfani da wasu bangare na dabbobin dan yin magani ba.

Masu sukar lamiri da rajin kare dabbobi sun ce janye haramcin na nufin za a sanya rayuwar ragowar dabbobin da suka rage a raye cikin hadari.

Hukumar da ke sa ido kan walwalar dabbobi ta duniya ta yi kira ga China ta sake nazari, saboda tamkar an bai wa masu farautar dabbobin ba bisa ka'ida ba lasisin cin karensu babu babbaka.

Su ma masu kasuwar bayan fage an ba su damar saidawa a sarari maimakon a baya da suke tsoron aikata hakan sai a kebantaccen wuri.

Wani bincike da aka gudanar ya yi hasashen damisa dubu hudu ne kadai suka rage a duniya, ya yin da karkanda ba zai gaza sama da dubu talatin.

Haka kuma a kasar Afirka ta Kudu masu fataucin haure ba bisa ka'ida ba na kashe akalla karkanda 20 a kowanne mako.