'Dole Saudiyya ta bayyana inda gawar Khashoggi take'

Marigayi Jamal Khashoggi
Bayanan hoto,

Batan dan jaridar ya janyo zanga-zanga a kasashen duniya

Shugabar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet na matsawa kasar Saudiyya lambar ta bari masu bincike na kasashen waje su shiga tawagar da ke binciken mutuwar dan jarida Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakandancinta da ke Santanbul na Turkiyya.

Miss Bachelet ta kuma bukaci hukumomin Saudiyyar su bayyana inda gawar mamacin ta ke don a samu damar gudanar da bincike akan ta.

Mai magana da yawun hukumar Ravina Shamdasani ta bayyana damuwar da suke yi kan batun, ta kuma ce bai kamata a bar Saudiyya ta gudanar da binciken ita kadai ba.

Hukumar ta yi kira ga kasashen Turkiyya da Saudiyyar su bada hadin kai wajen binciken, sannan hukumomin Saudiyya su fadi inda gawar mista Khashoggi take, saboda duk wani bincike ba zai kammalu ba tare da an yi kwakkwaran bincike kan gawarsa ba.

Masu bincike a Turkiyya sun nace da son bari su bincika wata rijiya da ke gidan diflomasiyyar Saudiyya wanda ba shi da nisa da ofishinsu, amma har yanzu hakan ba ta yiwu ba.

Yayin da jami'an suka ce an nade gawar a cikin wata darduma tare da bai wa wani da ba a bayyana ko waye ba don ya jefar.

Har yanzu dai ana diga ayar tambaya kan mutane 15 'yan Saudiyyar da suka isa Turkiyya a lokuta mabanbanta a ranar da aka kashe mista Khashoggi, wanda kuma suka shiga ofishin diflomasiyyar tare da barin kasar kasa da sa'o'i 48 da zuwansu.