'Hare-haren ta'addanci sun karu a Amurka da Turai'

An fi kai hare-hare da bama-bamai a yanzu fiye da shekarun baya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An fi kai hare-hare da bama-bamai a yanzu fiye da shekarun baya.

Wani bincike da aka gudanar a Turai ya gano cewa an samu karuwar hare-haren cikin gida na ta'addanci a masu tsananin kishin kasa ke kai wa a cikin 'yan shekarun nan.

Binciken wanda kungiyar da ke nazari kan rikice-rikice ta Think-tank a Birtaniya ta gudanar ya ce hare-haren ta'addanci sun lunka a Amurka da Turai da Australia tsakanin 2016 zuwa 2017.

Sakamakon binciken ya ce an fi kai hare-hare da bama bamai a yanzu fiye da shekarun baya.

Kuma binciken ya ce adadin mutanen da aka kashe sakamakon hare-haren ta'addanci na masu kishin kasa a fadin duniya ya karu.

Binciken ya bayyanna damuwa kan yadda cikin kashi hudu ne kawai na wadanda ke aikata laifukan hukumomi suka san da su.

Sakamakon binciken na zuwa bayan harin da dan bindiga ya kai a wurin bautar Yahudawa birnin Pittsburgh na Amurka inda ya kashe mutum a ranar Asabar.

Harin na ranar Asabar shi ne irinsa mafi muni da aka taba kai wa Yahudawa masu bauta a tarihin kasar.