Rikicin 'yan Shi'a: Sojoji da 'yan sanda sun yi amfani da karfi kan 'yan Shi'a.

Jami'an tsaron Najeriya
Bayanan hoto,

Ba wannan ne artabun jami'an tsaro da mabiya darikar Shi'a a Abuja ba, wadanda ke kiran a saki jagoransu Ibrahim El-Zakzaky da ake tsare da shi tun shekarar 2015

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta zargi sojoji da 'yan sandan Najeriya da amfani da karfi fiye da kima wajen tunkarar mabiya mazahabar Shia a yayin da suke zanga-zanga a birnin Abuja.

Amnesty International ta dora laifin mutuwar akalla mutane 45 na mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi ta 'yan shi'a a kan jami'an tsaron Najeriya a zanga-zangar kwanaki uku da suka yi suna gudanarwa a = Abuja.

Kungiyar ta ce bincikenta da ta gudanar ya nuna cewa amfani da karfin da ya wuce kima da sojoji da 'yan sandan Najeriya suka yi ne ya kai ga rasa rayuka da dama.

Amnesty ta ce jami'anta masu bincike sun ziyarci wurare guda biyar a Abuja da kuma cikin jihar Nasarawa inda mabiya Shi'a da suka ji rauni ke karbar magani, da kuma wurare biyu da aka ajiye gawawwakin wadanda suka mutu.

Kungiyar ta ce jami'anta sun tattauna da wadanda rikicin ya rutsa da su da kuma jami'an lafiya tare da yin nazari ga hotuna da bidiyo na wadanda suka ji rauni da wadanda aka kashe a lokacin zangar-zagar a ranar Asabar da kuma Litinin.

Babban daraktan kungiyar a Najeriya Osai Ojigho ya ce hotunun sun nuna yadda jami'an tsaro suka tarwatsa gangamin 'yan Shi'a ta hanyar bude wuta ba tare da wani gargadi ba wanda ya ce ya sabawa dokar Najeriya da ta duniya.

Amnesty ta ce akalla masu zanga-zanga 122 suka ji rauni ta hanyar harbin bindiga yayin da kuma 39 suka mutu a artabun da aka yi tsakanin jami'an tsaron da mambobin kungiyar 'yan uwa musulumin da ke zanga-zanga.

Amnesty ta kara da cewa ta na da shaidun da suka nuna 'yan sanda sun yi harbin kan mai tsautsayi, alhalin masu zanga-zangar ba sa dauke da makamai.

Amma a bangaren gwamnati Ministan tsaron Najeriya, Birgediya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya ce sojoji ba su yi amfani da karfin da ya wuce kima ba wajen tunkarar daruruwan 'yan shia'ar, inda ya zargi 'yan kungiyar da daukar doka a hannunsu tare da kokarin dibar makaman gwamnati.

Amnesty ta yi kira ga hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan hakan, tare da hukunta jami'an tsaro da suka bude wa 'yan Shi'ar wuta da kuma kwamandan da ya ba su umarni.