Najeriya na cikin kasashen da 'Yan jarida ke fuskantar barazana

An kashe 'yan Jarida sama da 1000 tsakanin 2006 zuwa 2017

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An kashe 'yan Jarida sama da 1000 tsakanin 2006 zuwa 2017

Najeriya ce kasa ta 13 a cikin jerin kasashen da 'yan Jarida ke fuskantar barazana a duniya.

Hukumar bunkasa ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta ware ranar ranar 2 ga Nuwamba a matsayin ranar kare hakkin 'yan jarida a duniya.

An ware ranar ne domin kiran kawo karshen karkashe 'yan jarida da ake yi a fadin duniya.

A wannan rana ta 2 ga watan Nuwamba shekarar 2013 aka kashe wasu 'yan jarida ma'aikatan gidan Radiyon RFI na kasar Faransa, bayan sun gama hira da wani dan siyasa a garin Kidal na kasar Mali.

An ayyana ranar ne don kira ga kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya, musamman hukumar raya al'adu ta Majalisar wato UNESCO domin kare 'yan jarida daga hare-hare a yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Haka kuma a duk lokacin da aka samu an aikata laifi kan 'yan jarida da ya kunshi cin zarafi ko kisa, UNESCO na bukatar a tabbatar da an gurfanar da masu laifin don hukuntasu.

Wata kididdiga da wata kungiya mai fafutukar kare hakkokin 'yan jarida wato CPJ mai mazauni a birnin New York na Amurka, da ta ke fitarwa a duk shekara ta yi nazari kan kasashe 14 da ake kashe 'yan jarida kuma ba tare da an hukunta wadanda suka aikata laifin ba a duniya.

Najeriya ce a matsayi ta 13 da ake kashe 'yan jarida ba tare da an hukunta wadanda suka aikata laifin ba, duk da cewa kungiyar ta ce an samu ci gaba matuka idan aka kwatanta da shekarun baya.

An kiyasta cewa daga shekarar 2006 zuwa 2017 an kashe kusan 'yan jarida 1,010 a dalilin ayyukan da suke gudanarwa a fadin duniya.

Sannan kashi 9 cikin 10 na irin wannan kashe-kashe na wucewa ne ba tare da an hukunta wadanda suka aikata al'amarin ba, abin da ke kara sanya rayukan 'yan jarida cikin hadari.