Karin albashi: 'Yan fanso na son a tuna da su
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Karin albashi: 'Yan fansho na son a tuna da su

Latsa alamar lasifika a sama domin sauraren hirar Ibrahim Isa da shugaban 'yan fansho na Kano

'Yan Fansho a Najeriya sun bayyana cewa suna goyon bayan fafutukar da kungiyar kwadagon kasar ke yi ta neman naira dubu talatin a matsayin mafi karancin albashi domin karin da za a yi zai iya shafar rayuwarsu.

Ana dai dakon bangaren shugaban kasa ya yi nazarin yarjejeniyar da kungiyar kwadagon ta cimma da wani kwamitin gwamnati dangane da karin albashin naira 30,000 mafi kankanta.

Comrade Salisu Ahmed Gwale shi ne shugaban kungiyar `yan fansho na jihar Kano, kuma a tattaunawarsu da Ibrahim Isa ya ce su ma suna bukatar kari saboda abin da ake biyansu bai taka-kara-ya-karya ba.