An tilasta wa mai nakasa yin fitsari a kwalba a jirgi

Darren Belling (a dama), tare da abokinsa Hakkin mallakar hoto DARREN BELLING
Image caption Darren Belling (a dama), tare da abokinsa

Wani gurgu dan Australiya mai wasan motsa jiki ya ce an tilasta masa yin fisari a kwalba yayin da yake bulaguro a jirgin flyDubai bayan da aka gaya masa cewa ba zai iya shiga bayan gida ba.

Darren Belling, mai shekaru 52, ya shiga jirgin ne domin zuwa Finland a watan Oktoba don wakiltar Australiya a gasar cin kofin kwallon gora ta kankara.

Mista Belling ya ce kamfanin jirgin saman ya fada masa cewa ba shi da keken guragu a jirgin, a yayin da jirgin ke zuwa Helsinki daga Dubai.

A wata sanarwa da FlyDubai suka fitar, sun ce ba za su iya samar da keken guragu ba a cikin jirgi.

Mista Belling ya ce ya tambayi masu aiki a cikin jirgi cewa yana bukatar keken guragu sa'o'i uku na tafiyar.

"Sai suka ce ba mu daukar keken guragu a cikin jirgi', suka gaya mani in rike fitsarin har sai an isa kuma tsawon tafiyar sa'a bakwai ne.

Bayan ma'aikatan sun tattauna, sai suka kawo masa kwalba domin ya yi fisari a ciki daga inda ya ke zaune.

Yawancin kamfanonin jiragen sama suna da keken guragu a cikin jirgi wadanda za su iya zazzagayawa a cikin jirgin.

Mista Belling ya ce flyDubai sun kuma yi kokarin cazar sai domin bargon da ya bukata don ya rufe jikinsa.

Ya shaida wa BBC cewa "Rashin karamcin da suka nuna mani ya bani mamaki."

FlyDubai sun ce ba za su ce komai a kan lamarin ba har sai sun yi magana da Mista Belling.

Labarai masu alaka