Masu ikirarin jihadi sun yi wa malamai bulala

Masu ikirarin Jihadi suna so makarantu da ke arewancin Burkina Faso su watsar da boko. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu ikirarin Jihadi suna so makarantu da ke arewancin Burkina Faso su watsar da boko

Makarantu a Burkina Faso da ke kusa da kan iyakokin Mali da Nijar suna samun barazana daga masu ikirarin jihadi cewa makarantu su watsar da ilimin boko.

A ranar Litinin, wasu maza hudu masu dauke da makamai a kan babur sun kai hari a wata makaranta da ke wata karamar al'umma a arewancin Toulfé.

Ministan Ilimi na Burkina Faso, Stanislas Ouaro, ya shaida wa BBC Afrique cewa 'yan bindiga sun tilastawa kowa sauka kasa kafin suka fara yi wa malamai hudu da daraktan makarantar bulala a gaban dalibai.

Ya kara da cewa daraktan ya sha bulala shida sai kuma aka yi wa malaman bibbiyu.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun bayyana kansu a matsayin mambobin Ansarul Islam, wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi da Malam Dicko ya bude a shekarar 2016, kuma ayyukansu na karuwa a arewacin kasar.

A halin yanzu, an rufe wata makarantar gwamnati a wannan makon a garin Gayeri da ke gabashin kasar, bayan malamai sun kai karar cewa sun ga wani sakon barazana da aka rubuta da Faransanci a kan wani allo na makarantar.

Ministan ilmi ya ce a sakon barazanar, an rubuta cewa: "Za mu sake dawowa ranar 14 ga watan Nuwamba don kwashe duka daliban makarantar." Idan muka samu malami a wajen, to ya mutu kawai."

Ministan ya shaida wa BBC cewa, an rufe fiye da makarantu 560 a yankunan kan iyakar tun watan Oktoba saboda malamai sun gudu ko ba sa zuwa aiki saboda matsalolin tsaro.

Labarai masu alaka