Masarautar Kano ta yi fiye da shekara 2000 da kafuwa
- Yusuf Yakasai
- BBC Africa, Abuja

Asalin hoton, Getty Images
Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero
An fara wallafawa wannan makalar ce a watan Disambar 2018
Wannan makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko tambayoyinku a kan tarihin masarautar Kano. BBC ta dauki lokaci don samo amsar tambayoyin daga wajen masana tarihi na masarautar Kano.
Masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a kasar Hausa a yammacin Afirka.
Tarihi ya nuna tsohuwar masarauta ce da aka kafa shekaru aru-aru tun zamanin jahiliyya kafin zuwan addinin Islama.
Masarautar ta taimaka wajen bunkasa garin Kano da Arewa da ma Najeriya baki daya.
Garin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a yankin arewacin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da garin.
Asalin Kalmar 'Kano'
Mutanen da suka fara zama a Kano makera ne da suka tashi daga garin Gaya domin neman kasa mai arzikin tama, wacce za su sarrafa su yi karfe da ita.
Mutanen sun yi dace da samun kasar mai kunshe da sinadarin tama, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta.
Wajen ya kuma kasance mai matukar tsaro kasancewar akwai manyan duwatsu da tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake idan an kai musu hari.
Duwatsun su ne dutsen Dala da Goron Dutse da Fanisau da Jigirya da Magwan.
Akwai kuma koguna daban-daban da suka kewaye yankin, da suka hada da kogin Jakara, da kuma kogin Kano.
Hakan ya sa mutane da dama suka ringa yin kaura zuwa yankin domin zama.
Asalin hoton, Sani Maikatanga
Sarki Ado Bayero a keken doki lokacin da ba ya iya hawa doki saboda tsufa da kuma rashin lafiya
Daga cikin mutanen da suka fi shahara cikin wadanda suka fara zama a yankin akwai wani jarumin mafarauci da ake cewa Kano, kuma sunansa ne aka sanya wa garin na Kano.
Masanin Tarihi Dakta Tijjani Muhammad Naniya ya ce har kawo yanzu masana ba su kai ga tantance lokacin da aka fara zama a yankin na Kano ba.
Sannan a cewarsa, masana basu gama tantance mutanen wace Gaya ce suka fara zama a yankin na Kano ba. Ya ce akawai Gaya ta Kano da ta Nijar da kuma ta yankin Sakkwato.
Babu cikakken bayani kan lokacin da aka fara zama a yankin Kano, amma a cewar Dakta Naniya an taba gano wata makera a kusa da dutsen Dala da masana suka ce ta kai shekara 200 bayan Annabi Isa.
Hakan ya sa ake hasashen cewa garin Kano ya kafu kimanin shekaru 400 kafin addinin musulunci. Ma'ana a yanzu birin ya kai shekara kusan 2000 da kafuwa.
Sarautar Kano
Asalin hoton, Kassim Turaki
Masu busa kakaki da masu algaita a wajen fadar Sarkin Kano, yayin da ake zaman fadanci.
A lokacin da aka kafa garin Kano babu wani shugaba guda daya da ya hada kan jama'a a karkashin mulkinsa.
Jama'ar da suke zaune a kauyuka kamar Dala da Goron Dutse da Fanisau da Magwan da Jigirya duk suna karkashin shugabanci ne na mutanen da suke tare da su.
Daga baya ne da garuruwan suka fara bunkasa, sannan dangantaka tsakaninsu ke kara inganta a lokacin ne aka samu shugaba guda daya da ya hada kan mutanen.
Barbushe
Barbushe, wani shahararren mafarauci ne da masana tarihi suka ce shi ne mutum na farko da ya hada kauyukan a karkashin ikonsa a lokaci guda.
Barbushe ne ya kuma kafa shugabancin Kano.
Masana tarihi na cewa Barbushe jika ne na kimanin 15 ga mutumin da ya fi shahara cikin wadanda suka fara zama a garin, kuma aka bai wa birnin sunansa wato Kano.
DaktaTijjani Naniya ya ce masana tarihi sun fi karkata ga cewa Barbushe shi ne mutumin da ya fara hada kauyukan Kano waje daya ta fuskar shugabanci da kuma addini.
"A lokacinsa ne addinin bautar Tsumburbura ya shahara, kuma Barbushe shi ne babban bokan Tsumburbura. Sha'anin addini shi ne babban abin da ya fara hada kan mutanen Kano."
Bayan zamanin Barbushe da kimanin shekara 200 aka samu wasu mutane daga yankin Daura da suka ci Kano da yaki suka kafa sarauta a karkashin Bagauda a shekarar 999.
Sarakunan Kano
Asalin hoton, Kassim Turaki
Sarkin Kano Usman II yana jiran isowar Yarima Edward dan sarauniyar Ingila a ziyarar da ya kai zuwa Kano a 1925.
Masana sun hadu cewa akwai gidaje da dama da suka yi mulkin Kano tun daga 999 zuwa yanzu.
Masanan sun ce tun daga kan Sarki Bagauda dan Bayajidda har kan sarkin Kano na karshe kafin fulani wato Sarki Alwali dukkaninsu daga jini daya suke.
Sai dai an ci gaba da samun sauye-sauye a tsarin shugabancin da kuma rungumar wasu sabbin abubuwa.
Masarautar Kano ta rabu ne zuwa gidaje biyar kamar haka:
- Gidan Bagauda
- Gidan Rumfa
- Gidan Kutumbawa
- Gidan Ibrahim Dabo
- Sarakunan Kano
Gidan Bagauda
- Bagauda dan Bawo, Jikan Bayajidda 999-1063
- Warisi dan Bagauda 1063-1095
- Gijimasu dan Warisi 1095-1134
- Nawata da Gawata 1134-1136
- Yusa 1136-1194
- Naguji 1194-1247
- Guguwa 1247-1290
- Shekarau 1290-1307
- Tsamiya 1307-1343
- Usmanu Zamnagawa 1343-1349
Sarakunan Kano da suka karbi musulunci
- Aliyu Yaji Dan tsamiya I 1349-1385
- Bugaiya 1385-1390
- Kanejeji dan Yaji 1390-1410
- Umaru 1410-1421
- Dauda I 1421-1438
- Abdullah Burja 1438-1452
- Dakauta 1452 ('Yan kwanki)
- Atume 1452 ('Yan kwanki)
- Yakubu dan Abdullahi 1452-1463
Asalin hoton, M T Safana
Hoton da ke nuna tsohon cikin gidan sarkin Kano (Gidan Rumfa) jim kadan bayan zuwan turawa. An dauki hoton gabanin a fara sauye-sauye na zamani a gidan
Gidan Rumfa
- Muhammadu Rumfa 1463-1499
- Abdullahi dan Rumfa 1499-1509
- Muhammad Kisoki (1509-1565)
- Yakubu 1565
- Dauda Abasama 1564 ('Yan Kwanaki)
- Abu-Bakr Kado 1565-1573
- Muhammad Shashere 1573-1582
- Muhammad Zaki 1582-1618
- Muhammad Nazaki 1618-1623
Gidan Kutumbawa
- Muhammadu Alwali Kutumbi 1623-1643
- Alhaji dan Kutumbi 1648-1649
- Shekarau II 1649-1651
- Muhammad Kukuna 1651-1652
- Soyaki 1652 (Ya yi mulki ne na wasu 'yan kwanaki)
- Muhammad Kukuna (An sake nada shi) 1652-1660
- Bawa (1660-1670)
- Dadi (1670-1703)
- Muhammad Sharif (1703-1731)
- Kumbari (1731-1743)
- Al-Hajj Kabe (1743-1753)
- Yaji II (1753-1768)
- Baba Zaki (1768-1776)
- Dauda Abasama II (1776-1781)
- Muhammad Alwali (1781-1805
Sarakunan da suka fi shahara
Asalin hoton, Kassim Turaki
Motar Sarkin Kano Sanusi na I a fadarsa
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Sarki Bagauda dan Bawo jikan Bayajidda da sarki Warisi dan bagauda da sarki Gijimasu da Warisi.
Wadannan ukun na farko sun shahara ne saboda su ne suka fara kafa mulkin birnin ya kuma tsaya har zuwa yau.
Masanin tarihi Dakta Naniya ya ce lokacin wadannan sarakunan ne aka fara ginin ganuwar Kano, domin ba ta kariya daga mahara.
Sarki Usmanu Zamnagawa, shi ma yana cikin wadanda suka shahara saboda ya yi juyin mulki, ya kashe sarki lokacinsa sannan tun daga nan ba a sake ganin sarkin ba, kuma ba a ga ko gawarsa ba.
Wasu na tunanin cewa ko ya cinye gawar sarkin ne, ko kuma binne shi ya yi, shi ya sa ma ake ce masa Zamna gawa.
Sai Sarki Yaji dan Tsamiya, 1349-1385 wanda a zamaninsa ne sarakunan Kano suka fara karbar musulunci, sannan ya yi kokarin tabbatar da ganin cewa musulunci ya zama addinin mutanen Kano.
A lokacinsa ne Wangarawa daga Tambuktu a karkashin Shiekh Abdurrahman Az-zagaiti (Az-zaiti) da ke kasar Mali suka ratsa ta Kano kan hanyarsu ta tafiya aikin hajji.
Ganin yadda garin ya ke, shi ne ya sa suka zauna suka yada addinin musulunci, sannan suka taimaka wa sarkin a yake-yaken da Kano ke yi da wasu yankuna, musamman Santolo, wato wajen Rano a yanzu.
Daga cikin Sarakunan da suka fi shahara akwai Muhammadu Rumfa, wanda ya taso da gidan Sarki daga kusa da dutsen Dala zuwa gidan Makama saboda cunkoso da aka fara samu a yankin a lokacin, da kuma yunkurinsa na samar da tsaro ga Sarki.
Sarki Rumfa ne ya gina gidan sarkin Kano na yanzu, kuma ya kawo sauye-sauye da dama a tsarin tafiyar da sarauta a Kano. A lokacin ne sarki ya fara zama kyam a kan karaga ba tare da yana motsi ba, kuma shi ne ya fara sunke, wato sarki ya yi amfani da gefen rawaninsa ya rufe bakinsa, don kar a ringa ganin lokacin da sarkin ya ke magana.
Sarakunan Fulani kuma kamar Sulaimanu, Ya fuskanci kalubale sosai daga wajen malamai da suka karbo tuta, amma duk da haka ya jagoranci Kano tare da jajircewa.
Ibrahim Dabo ci-gari, ya murkushe tawaye da dama, da kuma cinye garuruwa, sannan tun daga lokacinsa ne 'ya'yansa da jikokinsa suke sarautar Kano.
Abdullahi Bayero ya yi shuhura saboda abubuwa da dama da sauye-sauye na zamani.
Sarki Sanusi I shi kuma ya daidaita al'amura, da bunkasar Kano a Arewa da ma Najeriya.
Ado Bayero ya fi kowa dadewa a sarakunan Fulani, da kare mutuncin Kano, Ya yi zamani da gwamnoni 16.
Sarakunan da suka yi mulki daga Bagauda daga 999 zuwa 1807 sun shafe shekaru 808 kuma Sarakuna 43 ne suka yi mulki daga Bagauda zuwa Alwali.
Mulkin Fulani
Asalin hoton, M T Safana
Wani zane da ke nuna ziyarar da turawan Ingila suka kai wa Sarkin Kano Alu a fadarsa a 1900. Daga baya turawan sun koma suka ci Kano da yaki a 1903, suka kama Sarki Alu saboda ya ki mika wuya.
Asalin Fulani a Kano kamar yadda masanin tarihi Dakta Tijjani Naniya ya ce sun zo ne lokaci mai tsawo daga wasu kasashe na yammacin Afirka, da suka hada da yankin fulanin na Futa Jalo da kuma Futa toro.
Yankin ya hada da kasashe kamar su Gambia da Tumbuktu da Senagal, wato inda asalin kogin Kwara ya fara.
Fulanin sun kasu kashi biyu. Fulanin Soro, da suke yada ilimi da kuma addinin musulunci. Sai kuma makiyaya wandada suke tafiya da dabbobinsu domin kiwo.
Fulani sun je kasar Hausa a lokacin Sarkin Kano Abdullahi Burja (1438-1452). Kimanin shekara 400 kafin jihadin Shaikh Usmanu Dan Fodiyo.
Sai dai tun zuwansu ba su damu da shiga harkokin mulki ba.
Fulanin sun fara shiga harkokin mulki ne sakamakon kyamatar wasu al'adu da ake yi a kasar Hausa da suka saba wa addinin musulunci.
Galabar Shikh Usman Dan Fodiya a Sakkwato, ita ce ta bai wa sauran malaman Fulani da suke zaune a kasar Hausa karfin gwiwar cewa su ma za su iya yin nasara idan suka kalubalanci sarakunansu.
Gidajen Fulani Hudu ne suka yi yaki suka karbe mulki daga Sarakunan Hausawa a Kano, wato Dambazawa da Yolawa da Jobawa da Sullubawa.
Sarkin Kano na farko Malam Sulaimanu yana cikin fulanin Mundubawa wadanda ba sa cikin wadanda suka yi jihadi.
A bayansa kuma an dauko ne daga Sulubawan Dabo, ba bangaren Danzabuwa ba, wadanda suka yi jihadi.
Wani masanin tarihin masarautar Kano Malam Ibrahim Husain ya ce wadannan gidajen hudu su ne suka kafa sabuwar Kano bayan jihadi. Kuma su ne suke zabar sabon sarki a Kano idan wani sarkin ya mutu.
Daga baya kuma aka kara gidan Yalligawa da Jalligawa daga sarakunan Dutse da suka taba yin sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta a cikin masu zabar sarki.
A yanzu, gidaje biyu ne suke yin sarautar Kano tun bayan zuwan turawa, wato gidan Sarki Abbas, ko gidan Usman na biyu. wadanda dukkansu 'ya'yan Sarki Abdullahi Maje Karofi ne, shi kuma dan Ibrahim Dabo.
Sarakunan Kano na Fulani bayan jihadi
- Suleimanu dan AbaHama 1805-1819
Gidan Dabo
- Ibrahim Dabo dan Mahammadu 1819-1846
- Usman I Maje Ringim dan Dabo (1846-1855)
- Abdullahi Maje Karofi dan Dabo (1855-1883)
- Muhammadu Bello dan Dabo (1883-1893)
- Muhammadu Tukur dan Bello (1893-1894)
- Aliyu Babba dan Abdullahi Maje Karofi (1894-1903)
Sarakunan Fulani bayan zuwan turawa
Asalin hoton, M T Safana
Ranar da Turawa suka ci Kano da yaki suka kafa tutar Birtaniya a daya daga kofofin shiga garin.
- Muhammad Abbas Dan Maje Karofi (1903-1919)
- Usman II dan Maje Karofi (1919-1926)
- Abdullahi Bayero Dan Abbas (1926-1953)
- Muhammadu Sanusi I Dan Bayero (1954-1963)
- Muhammad Inuwa Dan Abbas (1963 - Tsawon wata uku kacal ya yi)
- Ado Bayero Dan Abdullahi Bayero (1963-2014)
- Muhammadu Sanusi II 2014 -
Masanan tarihi sun tabbatar da cewa ko a lokacin da fulani suka yi jihadi a Kano, sarkin lokacin Aliyu Yaji yana daga wadanda suka taimaka wajen yada addinin Musulunci a Kano da kawar da munanan al'adu da suka sabawa addinin musulunci.
Ana yi masa kallon mai kishin musulunci.
Misali, shi ne ya rusa wata al'ada ta mutanen Kano a lokacin da ake cewa Dirki. Wani tarin shara ne a wajen babban masallacin juma'a na Kano da ke kusa da gidan Sarki.
Mutanen Kano na lokacin a nan suke tara fatun dabbobin layya. Mutane sun mayar da wajen tamkar wani wajen tsafi da suke ganin duk wanda ya yi addu'a a wajen bukatarsa za ta biya.
Sarki Yaji ya hana wannan camfi da ake yi, sannan ya sa aka baje wajen ya kuma kawar da al'adar.
Dakta Tijjani Naniya ya ce babban abin da ya sa Sarki Alwali ya samu matsala da masu jihadi shi ne rashin amincewa da abin da suke yi.
Hakan ta sa suka fafata yakoki da dama har daga karshe Fulani masu jihadi suka kama shi bayan ya gudu daga Kano shi da mutanensa.
Wannan shi ne ya kawo karshen shekara 808 da Hausawa suka shafe suna mulkin Kano, kuma farkon mulkin Fulani a kasar ta Kano a 1903.
Asalin hoton, M T Safana
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II lokacin da Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta kai masa ziyara a gidan Sarki a 1956
Dalilin Sarki mai daraja ta daya?
Gabanin zuwan turawa babu bambamcin daraja tsakanin Sarakuna, sai dai a daular Sakkwato an amince cewa Sarkin Musulmi shi ne jagora.
Amma a lokacin da turawa suka zo sun raba garuruwan da suka mamaye zuwa larduna. Kuma ko wane lardi yana karkashin sarki mai daraja ta daya, da kuma wasu sarakunan masu darajoji hawa-hawa.
Asalin Tagwayen masu?
Tagwayen masu wasu masu ne guda biyu da suke a hade kuma yanzu ya zama shi ne abu mafi mahimmanci a gidan sarautar kano wanda yake nuna duk wanda ya mallake su shi ne Sarki.
Babu wanda zai rike Tagwayen masu kuma ya yi amfani da su sai Sarkin Kano.
Kuma kaf masarautun da ke karkashin daular Usmaniyya da ma ta Hausa ba wanda ke da hurumin amfani da su in ba gidan sarautar kano ba.
Sarkin da ya fara rike tagwayen masu?
Asalin hoton, Masarautarkano/instagram
Sarkin Kano Ado Bayero rike da Tagwayen Masu
Bayan mutuwar Sarki Gajimasu a shekara ta 1133 sai tagwayen 'ya'yansa Nawata da Gawata suka gaje shi. Tagwayen sarakuna lokaci daya akan karaga.
Launin mashin da kowanne daga cikinsu ke rikewa ya banbanta. Daya yana da launin ja wanda yake nufin ubangijin yaki. Dayan kuma yana da launin kore, wanda yake nufin ubangijin yabanya, kamar yadda wani jinin gidan sarautar Kano mai binciken tarihin masarautar Kasim Tijjani Turaki ya bayyana.
Asalin hoton, Masarautarkano/Instagram
Sarki Sanusi Rike da Tagwayen Masu da rawani kunne biyu
Sarakunan sun yi mulki ne na tsawon shekara biyu. Wasu masana tarihin na cewa daya daga cikinsu ne ya fara mutuwa, sai dayan ya hade masun guda biyu yake rike wa. Sun yi mulki ne gabanin zuwan addinin musulunci.
To sai dai wasu masana tarihin na cewa sun mutu ne lokaci daya, kuma bayan mutuwarsu ne kaninsu Sarki Yusa ya gaje su a shekara ta 1135 inda ya hada wadannan masun waje daya ya rike su a matsayin tagwayen masu.
Ya mulki Kano tsawon shekara 58 kuma tun bayan rasuwarsa a shekara ta 1193 ba a sake dauko tagwayen masu ba sai lokacin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa a shekara ta 1462, a cewar Kasim.
Asalin Takalmin gashin jimina
Sarakunan Kano sun kwaikwayo amfani da takalmin gashin jimina ne daga sarakunan Borno, wadanda su kuma suka kwaikwayo daga sarakunan daular Usmaniyya ta Turkiya, a cewar Dakta Tijjani Naniya.
Ba wanda ke sa takalmin gashin jimina sai sarkin Kano, babu kuma wanda ke rike tagwayen masu sai Sarki.
Rawani mai kunne biyu
Asalin hoton, Sani Mai Katanga
Rawani mai kunne biyu ya samo asali ne a lokacin sarakunan Fulani. Kuma wasu bayanai na cewa rawanin yana nuna tamkar sunan Allah ne.
Kewayen rawanin yana nufin Hakuri, kunnuwan biyu kuna suna nufin lam guda biyu, ma'ana lillahi.
Sarakunan Fulani
Asalin hoton, M T Safana
Sarkin Kano Alu dan Abudallhi Maje Karofi jikan Sarki Dabo
Malam Sulaimanu dan Abu Hama
Lokacin da aka yi jihadi aka kori Sarki Alwali an nada Sulaimanu ne a matsayin Sarki na daya a daular Fulani.
Gabanin nada shi, shi ne limamin manyan gidajen da suka hadu suka yi jihadi. Kuma mafi karantar shekaru a cikinsu.
Sai dai a cikin manyan jagorin jihadin akwai wadanda suka fi shi ilimi sosai.
Sarkin Kano Ibrahim Dabo dan Mahammadu 1819-1846
Malam Ibrahim Dabo shi ne sarki na biyu a sarakunan Fulani kuma na 45 a jerin sarakunan Kano.
Masanin tarihi Malam Ibrahim Hussain ya ce lokacin da aka yi jihadi Malam Ibrahim Dabo yana Lapai a kasar Nupe yana karatun addini.
Bayan komawarsa Kano an nada shi limamin Galadanci, daga nan aka nada shi limamin Kano, sai kuma aka nada shi Galadiman Kano, wacce ita ce sarauta mafi girma bayan ta sarki.
Daga baya kuma da Sarki Sulaimanu ya mutu sai aka nada Malam Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano.
Ana yi masa kirari da Ci-gari, saboda yadda ya ci garuruwa da dama ya shigar da su cikin kasar Kano.
Daga cikin garuruwan akwai Karaye da Rano da Dambatta da Dutse da wasunsu.
Kuma tun daga wancan lokacin har zuwa yau, 'ya'yansa da jikokinsa ne suke sarautar Kano.
Sarkin Kano Usman dan Ibrahim Dabo 1846 - 1855
Asalin hoton, Masarautarkano/instagram
Usman dan Ibrahim Dabo shi ne sarki na uku a sarakunan Fulani, kuma na 46 a jerin sarakunan Kano.
An nada shi sarautar Kano bayan mutuwar mahaifinsa. A lokacinsa ne "Babban Daki" ya samo asali, saboda ya gina wa mahaifiyarsa mai suna 'Shekara' gida ya mayar da ita ciki.
Asalin hoton, Masarautarkano/Instagram
Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya durkusa a gaban mahaifiyasa (Mai Babban Daki) yana gaishe ta yayin ziyarar da yake kai mata.
Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi Dan Dabo (1855-1883)
Malam Abdullahi, shi ne sarkin Kano na hudu a jerin sarakunan Fulani, kuma na 47 a sarakunan Kano.
Sarkin kano Abdullahi ya kawo sauye-sauye da dama a lokacinsa. Kamar kafa baitulmali inda ake ajiye kudin hukuma don taimaka wa gajiyayyu da musakai da gudanar da sauran bukatu na daular musulunci.
Sarki Abdullahi Maje karofi ya yi fama da tawaye na wasu sassan fulani da kuma yake-yake da wasu sarakuna.
Sarki Abdullahi Maje Karofi jarumin sarki ne, Kano ta bunkasa a zamaninsa, musamman ta hanyar cinikayya. Ya kuma bayar da muhimmanci wajen harkokin addinin musulunci.
Ya zartar da hukunce-hukunce ga wadanda aka samu da laifi.
Ya rasu a shekara ta 1882 a Karofi ta jihar Katsina yayin da zai tafi Sakkwato kai wa Sarkin Musulmi ziyara kamar yadda ya saba a kowace shekara.
Muhammadu Bello dan Ibrahim Dabo 1883-1893
Muhammadu Bello shi ne sarki na 48 a sarakunan Kano kuma na biyar a jerin sarakunan Fulani.
Sarki Bello Malami ne sosai wanda ya yi rubuce-rubuce na addini.
Sai dai a lokacinsa ya yi sauye-sauye a tsarin Sarautar Kano, musamman yunkurinsa na ganin cewa dansa Tukur ya gaje shi.
Asalin hoton, Masarautarkano/instagram
Sarkin Kano Sanusi ranar Sallah
Wasu masana tarihi na ganin wannan ne ma ya haifar da yakin basasar Kano tsakanin 'ya'yan Sarki Abdullahi Maje Karofi da kuma 'ya'yan kaninsa Sarki Bello.
An rasa daruruwan rayuka sakamako yakin da aka yi a lokacin.
Sarkin Kano Tukur 1893-1894
Sarkin Kano Tukur dan Muhammadu Bello shi ne sarki na 49 a sarakunan Kano kuma na shida a sarakunan Fulani.
Ya gaji mahaifinsa a matsayin Sarkin Kano, sakamakon nadin da Sarkin Musulmi Abdurrahman Danyen Kaso ya yi masa a 1893.
'Yayan Sarkin Kano Maje Karofi ba su amince da nadin da aka yi masa ba, don haka suka fita daga kano suka tattaru a Takai, inda suka shirya suka koma Kano aka yi yakin basasa, wanda a yakin aka kashe Tukur.
Yakin Basasa
Akwai dalilai da dama da suka janyo yakin basasa a Kano a cewar Dakta Naniya, inda ya ce babba cikin dalilan shi ne ajiye tsarin yadda ake zabar sarakunan Kano.
Lokacin da Sarkin Kano Muhammad Bello dan Ibrahim Dabo ya ke mulki ya nemi masarautar Sakkwato ta goyi bayan a nada dansa a matsayin Sarki, bayansa.
Hakan kuwa ya saba wa tsarin da ake bi wajen nada 'yayan Sarki Ibrahim Dabo, domin kuwa bayan mutuwar Dabo an nada 'ya'yansa ne Usman da Abdullahi Maje Karofi sai kuma Muhamadu Bello.
Kuma har a lokacin akwai sauran 'yayan Dabo, sannan akwai wadanda suka girmi Tukur a cikin jikokin Dabo.
Nada Sarki Tukur dan Muhammdu Bello a 1892 bisa goyon bayan Sakkwato ya fusata sauran 'ya'yan gidan sarautar Kano, musamman 'ya'yan Sarkin Abdullahi Maje Karofi.
Sun nemi cewa idan har za a fara nada jikokin Dabo ne a matsayin sarakunan Kano, to Yusufu dan Abdullahi Maje Karofi ya kamata a nada, domin kuwa shi ne babba a jikokin Dabo.
Wannan ya sa suka yi bore suka hada kai suka fita daga Kano suka yi sansani a Takai, daga baya suka shiga Kano aka yi yakin basasa, wanda a cikinsa aka kashe sarki Tukur a Tafashiya.
Sarkin Kano Alu Dan Abdullahi Maje Karofi 1894-1903
Sarki Aliyu Babba shi ne sarki na 50 a sarakunan Kano kuma na bakwai a sarakunan Fulani.
Ya zama sarkin Kano bayan sun yi nasara a yakin basasar da aka yi, kuma gabanin kammala yakin basasar cikin 'ya'yansa wanda shi ne shugaban Yusufawa wato Yusuf dan Abdullahi Maje Karofi ya mutu a Garko kafin su shiga Kano. Don haka sauran abokan tafiyarsu suka yi masa mubaya'a.
Asalin hoton, M T Safana
Alu ya zama Sarkin Kano yana da karancin shekaru kuma bai taba rike wata sarauta ba. Turawa ne suka sauke shi sannan suka kai shi Lokoja suka tsare shi a can da sauran Sarakunan da ba su mika wuya ga Turawa ba. Ya yi sarauta tsakanin 1894-1903. Nan yana zaune ne a Lokoja bayan sauke shi daga sarautar Kano.
Sarki Alu ya shahara sosai wajen jarumta, musamman a yakokin da Kano ta yi da wasu kasashe kamar Damagaram.
Ana yi masa kirari da Alu Mai Sango, saboda a lokacinsa ne sarakunan Kano suka fara amfani da Sango wato bindiga, wacce sarkin Nupe ya bashi.
Sango ya taimaka masa sosai wajen samun nasara a yake-yaken da ya yi.
A lokacinsa ne Turawa suka ci Kano da yaki, sannan suka kama shi suka kai shi Lokoja suka tsare shi a can har zuwa mutuwarsa.
Alu shi ne sarki na karshe gabanin zuwan Turawa.
Sarkin Kano Muhammadu Abbas 1909-1919
Asalin hoton, M T Safana
Sarkin Kano Abbas tare da hakimansa a bakin daya daga kofofin Kano jim kadan bayan turawa sun nada shi sarki na farko a zamaninsu
Turawa ne suka nada Muhammadu Abbas dan Abdullahi Maje Karofi a matsayin sarkin Kano bayan sun sauke kaninsa Aliyu Babba (Alu).
Abbas shi ne sarki na 51 a sarakunan Kano kuma na takwas a sarakunan Fulani.
Asalin hoton, M T Safana
Sarkin Kano Abbas yayin da ya kai wa turawa ziyara a mazauninsu da ke unguwar Bompai Kano
Bayan turawa sun ci galaba a yakin Kwatarkwashi kan hanyar Sakkwato sai Abbas ya jagoranci kanawa domin komawa gida don a yi sulhu da Turawa.
Shi ne ya jagoranci mika wuya ga turawa, kuma saboda wannan ne Lord Lugard ya nada shi sarki a watan Mayun 1903.
Don haka shi ne ya zama sarki na farko bayan zuwan Turawa.
Sarkin Kano Usman II 1919-1926
Asalin hoton, M T Safana
Sarki Usman II ya zama sarkin Kano yana da shekara 84 a duniya. Shi ne wanda ya fi kowa tsufa a sarakunan Kano lokacin da aka nada shi sarki. Shi ya sa ake ce masa Sarki Usman Dan Tsoho
Sarkin Kano Usman na biyu shi ne sarki na 52 a sarakunan Kano kuma na tara a jerin sarakunan Fulani.
A lokacinsa aka kafa sabuwar Kano da ta samu sababbin abubuwan ci gaban zamani.
A lokacinsa aka fara aikin samar da ruwan famfo da wutar lantarki.
A lokacinsa aka fara ginin Babban asibiti birni da kuma aiki titi.
Kuma a lokacinsa jirgi ya fara sauka a Kano da ginin filin jirgi sama wanda daga bisani aka kammala wananan ayyuka bayan mutuwarsa lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero.
A lokacinsa ne dan Sarauniyar Ingila Yarima Edward ya zo Kano a shekara ta (1925) wanda ma wasu ke gani shi ne lokaci na farko da jirgi ya fara sauka a kasar gaba daya. Kuma a lokacinsa aka fara hawan Durba ta sarakunan Arewa inda ya jagorance ta.
A tarihin masarautar Kano ba a taba sarki mai yawan shekarun Sarki Usman na II ba.
Ya yi sarki yana da shekara 77 a duniya, ya kuma yi shekaru bakwai yana mulki, sannan ya mutu yana da kusan shekara 84 a duniya a shekara ta 1926.
Saboda shekarunsa ne ake ce masa Sarki Usman Dan Tsoho.
Sarkin Kano Abdullahi Bayero 1926-1953
Asalin hoton, M T Safana
Sarkin Kano Abdullahi Bayero, mahaifin Sarki Sanusi da Ado Bayero. Shi ne ya fara zuwa aikin hajji a sarakuna Kano
Sarki Abdullahi Bayero shi ne sarkin Kano na 53 a jerin sarakunan Kano, kuma na 10 a jerin sarakunan Fulani.
Sarki Bayero yana daga cikin sarakunan Kano da suka fi shahara. Ya yi karatun addinin musulunci mai zurfi, kuma ya yi mu'amala da wasu malamai na duniya.
A lokacinsa ne ruwan fanfo ya fara zuwa a Kano, haka kuma a lokacinsa ne aka fara saka wutar lantarki.
A lokacinsa ne aka bude asibiti na farko. Kuma a lokacinsa ne aka fara gina makarantun boko.
Asalin hoton, M T Safana
Sarkin Abdullahi Bayero ya kawo ci gaba da dama a lokacin mulkinsa
Shi ne Sarkin Kano da ya fara zuwa aikin hajji. Shi ya sa ma ake ce masa Sarki Alhaji.
Bayan ya dawo daga hajji ya tafi Masar inda ya ga wani mashahurin masallaci a can, don haka yana komawa Kano ya rushe tsohon masallacin birnin ya gina sabo a bisa tsari irin wanda ya gano a Masar.
Asalin hoton, Idris Sanusi
Sarki Abdullahi Bayero a dama da dansa Sarki Sanusi a lokacin yana Chiroman Kano
Sarki Muhammdu Sanusi I 1953-1963
Asalin hoton, Kassim Turaki
Sarki Sanusi I da wasu daga cikin jikokinsa, cikin har da sarkin Kano mai ci Muhammadu Sanusi II
Shi ne babba a cikin 'ya'yan Sarki Abdullahi Bayero, kuma tun zamanin mahaifnsa, Muhammadu Sanusi yana da karfin fada a ji a fadar Kano.
Sarki Sanusi ya yi tasiri sosai a lokacin tsarin mulkin mallaka a Najeriya.
A lokacinsa ne Saruaniyar Ingila Elizabeth II ta kai ziyara Najeriya a 1956.
Tun kafin ya zama sarkin Kano babban amini ne ga Sardaunan Sakkwato Ahamdu Bello wanda shi ne Firimiyan jihar Arewa. Amma daga baya an samu sabani tsakaninsu.
Sabanin ya kai har an kafa wani kwamiti domin ya binciki Sarki Sanusi kan wasu ayyuka a Kano. Kuma daga karshe matsalar har ta kai ga an sauke Sarki Sanusi daga sarautar Kano.
Sai dai wasu na ganin da kansa ya yi murabus domin tsira da mutuncinsa.
Asalin hoton, M T Safana
Sarki Sanusi ya kawo Sauye-Sauye a Kano zamanin mulkinsa
Bayan ya bar sarauta ya koma garin Azare na jihar Bauchi da zama, sannan daga baya gwamnatin Abubakar Rimi ta mayar da shi garin Wudil inda ya mutu a can.
An nada shi Sarki bayan mutuwar mahaifinsa a 1953. Sarkin Sanusi ya kasance mai kwarjini da kasaita a lokacin da yake Sarauta.
Ya kawo sauye-sauye da dama a sarautar Kano, ya kuma yi gyare-gyare da dama a gidan sarautar Kano.
Bayan saukarsa daga Sarkin Kano, Shaikh Ibrahim Inyass ya nada shi Khalifansa a Najeriya da Afirka ta yamma.
Asalin hoton, Idris Sanusi
Sarki Sanusi I a karshen rayuwarsa bayan ya koma Wudil da zama
Kafin ya zama sarki, Sanusi ya zama dan majalisar jihar Arewa a 1947, sannan yana daga cikin wadanda suka karfafa jam'iyyar NPC a Arewa.
Sarki Sanusi malami ne na addinin musulunci, a lokacinsa shi ne yake limanci, kuma yana zartar da shari'a.
Sarki Inuwa Abbas 1963
Asalin hoton, M T Safana
Sarki Muhammadu Inuwa ya yi mulki ne na tsawo watanni shida a 1963
Muhammadu Inuwa shi ne na 55 a jerin sarakunan Kano, kuma na 12 a jerin sarakunan Fulani.
An nada shi sarkin Kano bayan murabus din Sarki Sanusi I.
Kafin ya zama sarki ya riki mukamai daban-daban ciki har da Galadiman Kano.
Sai dai watanni shida kawai ya yi yana mulkin Kano sai ya mutu.
Sarki Ado Bayero 1963-2014
Asalin hoton, Masarautarkano
Ado bayero ya shafe shekara 51 yana mulkin Kano
Sarki Kano Ado dan Abdullahi Bayero shi ne na 56 a jerin sarakunan Kano, kuma na 13 a jerin sarakunan fulani.
An nada shi sarki bayan mutuwar baffansa Sarki Inuwa Abbas. Ba ya cikin wadanda suka nemi sarauta a lokacin.
Yana cikin wandanda suka yi sarkin Kano ba tare da sun riki wata sarauta ba, kuma wadanda suka zama Sarki da karancin shekaru.
An zabi Alhaji Ado Bayero a matsayin dan majalisa mai wakilitar Kano a Majalisar dokoki ta Kaduna a 1954, inda ya zauna har zuwa shekaru uku.
A 1957 kuma sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya nada shi wakilin doka, wanda a lokacin yake daidai da babban jami'in tsaro na Kano, har zuwa 1952 lokacin da gwamnatin Najeriya karkashin Firaminista Sir Abubukar Tafawa Balewa ta nada shi jakadan Najeriya a kasar Senegal.
Asalin hoton, Masarautarkano/instagram
Sarki Ado Bayero ya yi zamani da shugabannin Najeriya tun daga wadanda suka karbi mulki daga turawa har zuwa kan Goodluck Jonathan. Ya rasu a 2014 bayan ya shafe shekara 51 yana mulkin Kano.
A ranar Juma'a 11 ga watan Oktoban 1963 ne aka nada Alhaji Ado Bayero a matsayin sarkin Kano bayan rasuwar Sarki Muhammad Inuwa dan Sarki Abbas.
Ya hau sarautar Kano yana da shekaru 33, sannan ya yi mulki na tsawon shekaru 51.
Alhaji Ado Bayero shi ne sarki mafi dadewa a sarakunan Fulani a kano da suka fara mulki bayan jihadi a shekara ta 1807.
Sarkin Ado Bayero ya rasu ranar 6 ga watan Yunin 2014, yana da shekaru 84 a duniya, ya kuma bar mata 4 da 'ya'ya sama da sittin da jikoki fiye da 300.
Asalin hoton, Dandalin Tarihin magabata/facebook
Ado Bayero yana yaro. Ya zama sakin Kano yana da karancin shekaru
Sarki Muhammadu Sanusi II 2014
Muhammadu Sanusi shi ne na 57 a jerin sarakunan Kano, kuma na 14 a jerin sarakunan Fulani.
An nada shi sarkin Kano bayan mutuwar Sarki Alhaji Ado Bayero.
Muhammadu Sanusi II jikan Sarkin Kano Sanusi I ne. Maihaifinsa Aminu Sanusi ya yi Chiroman Kano.
Asalin hoton, Sani Maikatanga
Sarkin Kano Sanusi II tsohon gwamnan Babban Bankin Najeiya ne
Shi ne sarkin Kano da ya fi magabatansa ilimin zamani, sannan kuma yana da ilimin addinin musulunci.
Kwararren masanin tattalin arziki ne, kuma kwararren ma'aikacin banki, inda ya taba rike mukamin gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN.
Asalin hoton, Masarautarkano/instagram
An sauke shi daga mukamin gwamnan CBN saboda yadda yake sukar gwamnatin Goodluck Jonathan da mulki a lokacin.
An haifi Muhammadu Sanusi II ranar 31 ga watan Yulin 1961. An nada shi Sarkin Kano ranar Lahadi 8 ga watan Yuni 2014.
Alakar Masarautar Kano da Darikar Tijjaniyya.
Asalin hoton, Idris Sanusi
Sarkin Kano Sanusi I da Shaikh Ibrahim Inyass babban jagoran darikar Tijjaniya
A lokacin Sarkin Kano Abbas ne wasu malamai na darikar Tijjaniya suka je Kano, kuma sun taimaka wa sarkin sosai da addu'o'i ta yadda zai ci nasara a kan abokan hamayyarsa, musamman wani waziri da aka yi da ake kira 'Alabar Sarki', kuma mai karfin fada a ji, wanda har ta kai ya kusan kwace sarautar Kano saboda karfin iko da turawa suka ba shi.
Haka kuma malaman sun taimaka wa Sarkin Kano Abbas wajen samun mafita daga tasirin yakin basasar da aka yi a Kano gabanin zuwa Turawa.
Daya daga cikin manyan malaman na Tijjaniyya shi ne Shariff Ujdud. Mafi yawan masana tarihi na cewa a lokacin sarki Abbas ya karbi darikar ta Tijjaniyya, kuma tun daga wancan lokacin har zuwa yau sarakunan Kano suna bin darikar Tijjaniyya ne.
Gabanin Sarki Abbas dai Sarakunan Kano tun bayan jihadi Suna bin darikar Kadiriyyya ne.
Asalin hoton, Masarutarkano/Instagram
Sarki Sanusi I yayin zikirin Juma'a na shekara-shekara da ake yi a gidan Sarkin Kano. Suna zaune da daya daga jikokin shehu Tijjani wanda ya kafa darikar Tijjaniya
Sai dai kuma wani bangare na masana tarihin masarautar Kano na ganin cewa sai a lokacin Sarki Abdullahi Bayero ne, sarakunan Kano suka fara karbar darikar Tijjaniyya. To amma wannan ra'ayi ba shi da karfi a wajen masana tarihi.
Alakar gidan Sarautar Kano da darikar Tijjaniyya ta kara karfi lokacin da Shariff Alawi ya zo Kano a 1923.
Alakar ta kara karfi lokacin da Sarki Abdullahi Bayero ya hadu da Shaikh Ibrahim Inyass a lokacin aikin hajji, musamman ma saboda ziyarar da Shaikh Inyass ya kai ziyarar farko a Kano a 1945.
Ko Borno ta taba cin Kano da yaki?
Masanin tarihi Dakta Tijjani Naniya ya ce bayanai sun nuna cewa Borno ta taba yin galaba a Kano a karni na 11 zuwa na 12 inda har Kano ta amince cewa za ta ringa aike wa Borno haraji domin ta zauna lafiya.