Ziyarar Blac Chyna Najeriya ta jawo ce-ce-ku-ce

Blac Chyna

Ana ci gaba da muhawara a kafafen sada zumunta musamman a Najeriya game da ziyarar da wata mai tallan kayan kawa da sayar da kayan kwalliya Blac Chyna za ta kai kasar.

Blac Chyna dai ta yi suna ne domin kayayyakin da take sayarwa da kuma mu'amalar da ta yi da Rob Kardashian, wato yayan wasu manyan masu tallan kawa a kasar Amurka.

'Yar shekara 30 din ta bayyana a shafin ta na Instagram cewa za ta kaddamar da sabon man shafawanta mai sauya launin fatan mutum wanda aka fi sani da man shafawa na Bleaching.

Ta gayyaci jama'a da su same ta a shagon man mai suna Whitenicious wanda yake a jihar Legas a ranar Lahadi.

Har ila yau, wasu jama'a sun ta sukar ta a kan cewa ziyararta ta farko nahiyar Afrika, "ba abin alheri ba ne zai kawo ta ba."

Wannan ya sa wasu mabiyanta a shafinta na Instagram suka yi ta zaginta a kan cewa tana da manufar koya wa mata yadda za su sauya halitar da Allah ya yi musu.

Tsokacin ya janyo har ta toshe mutane daga tura mata ra'ayoyinsu a shafinta na Instagram.

Wani ya bayyana ra'ayinsa game da batun kamar haka: "Me ya faru da kyan fatar bakake da kuma mutum yaso halittar da ubangiji ya yi maka."

Sai dai ta mayar musu da martani, inda ta ce ba man sauya launin fata ba ne, mai ne da ke gyara kyan jiki.

Wasu ma har suna mai da hankali akan cewa Blac Chyna ruwa biyu ce, kuma babanta baki ne - inda suka ce abin da ya sa ake kiranta da Blac Chyna ke nan, wato "Bakar 'yar China".

Wani abin kuma da mutane suke tsokaci a kai shi ne farasha man nata, man ya kai kimanin dala 250, kimanin naira dubu 100 ke nan.

"Abin haushin shi ne ba ma sayar da man sauyin launin fata da Blac Chyna za ta yi a Najeriya ba, abin haushin shi ne cewa farashin man ya kai dala 250, wato naira dubu 90.

"Kuma kun san mai? Mutane dole za su saya wanan man nata," in ji Sally.

Wasu sun rika kareta inda suke cewa man ya ci kudinsa, saboda a jikin kwalbar man akwai duwatsu masu daraja na kamfanin Swarovski.

A Najeriya dai masu siyar da man sauya launin fata sun saba shan suka, saboda manufar man da kuma tsadarsa, misali Bobrisky, wani mai siyar da irin man.

Shi ma ya sha suka a kwanan baya a kan mansa da yake siyarwa a farashin da ya wuce naira dubu dari.