'Mata na fuskantar cin zarafi a Tarayyar Afirka'

AUC
Image caption Ma'aikata mata da 'yan mata masu neman aiki lamarin ya fi shafa

Babban kalubalen da matan da ke aiki a kungiyar tarayyar Afirka ke fuskanta shi ne cin zarafi ta hanyar lalata kamar yadda wani bincike ya gano.

Yawancin ma'aikatan dai na wucin gadi ne da suka kunshi ma'aikatan sa-kai da masu neman aiki da sauransu.

Rahoton ya ce wadanda suke neman yin lalata da matan dai kan kira kansu da masu ruwa da tsaki da masu fada aji a hukumar.

A watan Mayu da ya wuce ne dai aka gudanar da binciken, kuma an yi nasarar jin ta bakin daukacin ma'aikatan da suka kai korafi tare da yi musu tambayoyi da alkawarin ba su kariya.

Shugaban hukumar tarayyar Afirka AU Moussa Faki shi ya kafa kwamitin domin gano bakin zaren bayan korafi ya yi yawa kan abin da ke faruwa.

Tawagar masu binciken sun tattaro bayanan mata daban-daban har 44 da suka fuskanci wani nau'i na cin zarafi daga shugabanni.

Lamarin ya fi kazanta ga matasan matan da suke zuwa neman aiki, inda ake sanya sharadin yin lalata da su kafin a sama musu aikin.

Ma'aikata matan sun ce babu yadda za su yi don a kan yi musu barazanar sallama daga aiki idan ba su bada hadin kai ba.

Ya yin da wasu kuma ake musu alkawarin kwantiragi mai tsoka musamman 'yan mata, rahoton ya ce ma'aikatan da aka zanta da su, sun ce lamarin ya munana ne saboda rashin daukar mataki ko wani hukunci da kungiyar tarayyar Afirka ta tanadar da za ta hukunta wadanda aka kama da laifin yin lalata ko ma yunkurin yin lalata da wata ma'aikaciya.

Masu binciken sun kuma gano yadda cin hanci da rashawa, da wulakanci, da barazana da nuna wariya suka yi katutu a AUC.

Sai dai rahoton bai bayyana sunayen mata ko shugabanni ko wadanda suka aikata laifin ba.

Labarai masu alaka