Iran ta zargi Amurka da hada yaki a yankin Larabawa

A makon da ya gaba Javad ya fuskanci bacin ran majalisar dokokin kasarsa
Image caption Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya yi suna wajen sukar Amurka

Ministan harkokin wajen Iran, Javad Zarif ya ce Amurka ta mayar da yankin Larabawa wani dandalin jibge makamai.

Javad ya kara da cewa "ma fi yawan makaman da Amurkar ke shigarwa yankin na Larabawa na zuwa hannun masu tsaurin addini kamar al-Qaeda a Yemen da IS a Syria".

A hannu daya kuma shugaban na Iran, Hassan Rouhani ya bayyana takunkuman da Amurkar ta kakaba wa kasarsa da ta'addanci ta fannin tattalin arziki.

Rouhani ya ce takunkuman sun zama tarnaki ga Iran wajen yakar safarar miyagun kwayoyi da kuma batun 'yan cirani.

Hassan Rouhani ya kuma yi gargadin cewa idan har ba iya wa tufkar hanci ba to akwai yiwuwar samun karuwar miyagun kwayoyi da 'yan cirani da ma hare-haren sojin sa kai a yankin na Larabawa.