Kwana 29: Abin da ba ku sani ba na rayuwar Atiku Abubakar #BBCNigeria2019

atiku

Asalin hoton, Getty Images

Daya daga jiga-jigan mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP, tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, mai shekara 72, matsin lambar takun-sakarsa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ce ta fara tursasa shi ya fice daga jam'iyyar.

Atiku Abubakar ya sha cewa ya samu dukiyarsa ne bisa iya juya jarin da ya zuba, ya kuma taki sa'a, kamar yadda ya fada a gaban kwamitin binciken da Obasanjo ya sa a yi, inda aka tuhumi mataimakin shugaban kasar da karkatar da akalar Dalar Amurka miliyan 125 daga asusun raya kasa zuwa harkokin hada-hadar kasuwancinsa.

Ko da yake Atiku Abubakar ya musanta zargin da aka yi masa, sannan ya mayar da mummunan martani tare da caccakar Shugaba Obasanjo, inda ya jefa zargin cin hanci a kansa, har ta kai ga wasu daga jerin batancin (da suka yi wa junansu) na ci gaba da kewayawa.

Har yanzu Atiku Abubakar zai yi matukar wahala ya iya shawo kan 'yan Najeriyar da za su kada kuri'a a zabe cewa kasancewarsa jami'in hana fasa-kwauri (kwastam) na tsawon shekara 20 ne ya ba shi damar kasancewa hamshakin attajiri, mai dimbin jari a hada-hadar man fetur da kafofin yada labarai da harkar dabi'i da harkokin ilimi.

Asalin hoton, Getty Images

Ya mallaki katafariyar jami'ar ABTI, wato American Unibersity of Nigeria a Jiharsa ta Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Kamfaninsa na hada-hadar man fetur, mai suna Intels' Nigeria Limited na hada-hada a kasashen Afirka da suka hada da Angola da Ekuatorial Guinea da Gabon da Sao Tome and Principe.

Sai dai Hukumar Yaki da Yi wa tattalin Arziki Ta'annati ta EFCC, wadda ta gudanar da binciken bibiyar kadin yadda Atiku Abubakar ya tafiyar da harkokin Asusun Raya albarkatun man fetur na PTDF ba ta gamsu da shi (hujjojinsa) ba.

'Sauya akalar mulki'

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Dimbin takaddamar shari'ar da mataimakin shugaban kasar ya fuskanta ta yiwu su suka dauke masa hankali, lokacin da Shugaba Obasanjo ya tattara hankalinsa wajen kokarin tabbatar da Umaru Musa Yar'Adua a matsayin magajinsa, a karkashin jam'iyyar PDP bayan ya sauka daga mulki

Wata Babbar Kotun Legas ta tabbatar da rahoton da ke tuhumar Atiku Abubakar da laifin cin hanci, ga kuma babbar matsala kan yadda zai fuskanci majalisar dattijai da kotu, al'amarin da ka iya haifar masa da cikas din tsayawa takarar shugaban kasa.

Mutane da dama na ganin mummunar sa-insar da ke tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa na hakikanin gaskiya ba ta dace ba, a cewar Adamu Hamza, wani mai nazari kan harkokin siyasa.

Sai dai samun damar tsayawa takara karkashin tutar jam'iyyar adawa ta AC a 2007, an yi hasashen Atiku Abubakar zai tunkari wata matsalar, wato karo da Muhamadu Buhari dan takarar Shugabancin kasa na Jam'iyyar ANPP, matukar dai zai yi takara a zaben Afrilu, bayan da aka gudanar da yarjejeniyar zabe a tsakanin jam'iyyun biyu.

"Mutum ne mai kankan da kai, magidanci mai tausayin al'umma, wanda ba ya mantawa da abokansa, a cewar mai Magana da yawunsa na wancan lokacin, Garba Shehu, kamar yadda ya bayyana wa BBC.

Asalin hoton, Getty Images

Ya ce jagoran koyinsa a fagen siyasa, shi ne Shugaban Amurka Bill Clinton.

"Clinton managarcin dan siyasa ne. Za ka iya cewa mutum ne mai sha'awar siyasa, kuma shi kawai mai sha'awar siyasa ne.

Atiku Abubakar ya yi hankoron ganin "sauya akalar mulki' - manufar dawo da mulki Arewa bayan Obasanjo, wanda ya fito daga Kudu, dan kudu zai goyi bayansa.

Sai dai shi ma tamkar Buhari da dan takarar PDP Yar'Adua, Atiku Abukar Bafullatani ne Musulmi, don haka tunaninsa na samun goyon baya ya kwaranye

Dawuda da Jaluta (Rarrauna ya samu galaba kan rarrauna)

Yana ganin kansa a matsayin jigon kafa dimokuradiyya, saboda fitowar da ya yi karara wajen adawa da sauya kundin tsarin mulki, don bai wa Shugaba Obasanjo damar sake tsayawa takara a zagaye na uku.

Magoya bayansa

Magoya bayan Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar, sun koka kan yadda aka tauye su, don matakin da Atiku Abubakar ya dauka ya sa ya yi farin jini a wajen 'yan Najeriya da dama, sai dai an yi hasashen ba lallai ne a kada masa kuri'u a zaben Afrilun 2007 ba, saboda wasu na ganin kawai ya zaku ne da son karbar mulki daga Obasanjo.

Sannan, wasu mutanen da ke bukatar sauyi bayan shekara takwas na Obasanjo za su yi taka tsantsan wajen ganin ba su fada hannun mataimakinsa ba, har na tsawon kwatankwacin lokacin.

Duk da haka, Takun-sakar Atiku da Shugaba Obasanjo tuni ya zama tamkar labarin Dawuda da Jalutta (mai rauni ya samu galaba kan kakkarfa), inda dimbin masu kada kuri'a ke tausaya wa mataimakin shugaban kasa, wanda suke gani a matsayin mutumin da aka zalunta

"Shugaban kasa na amfani da karfin ikon gwamnati, kuma mutane da dama na ganin mummunar matsin lambar shugaban kasa ga mataimakinsa, wanda suka kaddara a matsayin mai rauni (Dawuda), a wannan yanayin, bai dace ba, a cewar wani mai sharhi kan al'amuran siyasa, Adamu Hamza.

Idan har kudi za su yi tasirin sa mutum ya ci zabe, kamar yadda a wani lokacin sukan haifar da nasarar lashe zabe a Najeriya, to da tuni Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya.

Tarihinsa a takaice

An haifi Atiku Abubakar GCON ranar 25 ga Nuwambar 1946, ya kasance jigon dan siyasa kuma hamshakin attajiri a Najeriya.

Tun bayan da Najeriya dawo mulkin dimokuraxiyya cikin shekarar 1999, Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasar Najeriya na 11, a mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo a tsakanin 1999 zuwa 2007.

Asalin hoton, Getty Images

Tun cikin shekarar 1998 aka zabe shi Gwamnan Jihar Adamawa.

Daidai lokacin da yake a matsayin zababben Gwamnan, sai zababben shugaban kasa ya zabe shi don ya mara masa baya a matsayin mataimakin shugaban kasa.

An dai rantsar da su ranar 29 ga Mayun 1999 a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa bayan da suka lashe zabe a Fabrairun 1999.

Yunkurinsa na maye gurbin Obasanjo a karshen wa'adin mulkinsa ya ci tura bayan da ya yi ta yin takun saka tsakainsa da Obasanjo, sannan ya fuskanci kalubalen shari'a, har ta kai ga daga bisani suka karke a Kotun Koli ta Najeriya, wadda ta bai wa Hukumar zabe ta INEC umarnin sanya sunan Atikun a jerin 'yan takara.

Ya yi takarar shugaban kasa ta farko karkashin tutar jam'iyyar AC, bayan da ya fice daga jam'iyyar PDP, al'amarin da ya haifar masa koma-baya a zaben 2007, inda ya zo na uku, bayan Umaru Yar'Aduwa na jam'iyyar PDP da Muhammadu Buhari na Jam'iyyar ANPP.

Kasuwanci da masana'antu

A fannin kasuwanci da masana'antu kuwa, shi ne jigon kafa kamfanonin man fetur na Intels da ke gudanar da ayyukansa a Najeriya da wasu kasashen waje.

Sannan shi ya kafa kamfanin sarrafa kayan abinci na Adama Beverages, inda a fannin ilimi ya mallaki Jami'ar Amurka ta Najeriya, wato ABTI.

  • An haife shi ranar 25 ga watan Nuwambar 1946
  • Shekararsa 72
  • Bafulatani ne musulmi dan jihar Adamawa
  • Matansa hudu da yara da dama
  • Ya yi mataimakin shugaban Najeriya tsakanin 1999-2007
  • Ya yi takarar shugaban kasa sau biyu har da na 2019
  • Ya taba yin gwamnan Jihar Gongola

Sasantawar Atiku da Obasanjo

An yi ta ci gaba da samun takaddama tsakanin Obasanjo da tsohon matakimakinsa Atiku na tsawon shekaru har bayan komawa jam'iyyar APC da Atikun ya yi a 2015.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fitaccen malamai Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya sasanta Atiku da Obasanjo

Daga bisani bayan Atiku ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Muhammadu Buhari, sai kuma ya sake sauya sheka zuwa gidansa na farko wato PDP, yana mai alakanta hakan da "rashin iya mulkin Shugaba Buhari," a cewarsa.

A 2018 ne Atiku ya nuna sha'awarsa ta son tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019, kuma abun da ya bai wa kowa mamaki shi ne sake kullewarsa da Obasanjo, sakamakon sasanta su da aka yi karkashin jagorancin fitaccen malamai Sheikh Ahmad Mahmud Gumi.

A yanzu dai Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar PDP, zai fafata da abokin karawarsa Shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki a ranar 16 ga Fabrairun 2019.

Sauyin sheka

'Yan siyasa sun ta sauyin sheka a wannan karon bisa tunanin Atiku Abubakar zai saki makudan kudi, kamar yadda ya saba yi a baya.

Wannan karon dai daukacin ''yan takarar da ke da karfi a zaben bana, wato Atiku Abubakar da Shugaba Muhammadu Buhari babu wanda aka kwararo makudan kudi daga bangarensa, al'amarin da jaridun kasar suka bayyana cerwa yakin neman zaben bana bai yi armashi ba.

Kuma a ranar Alhamis din makon nan ne wani Daraktan yada labaran ofishin yakin neman zabensa, Mista Kola Ologbondiyan, ya bayyana dabarun yakin neman zaben Atiku, tare da alkawarin yaki da cin hanci da rashawa.

"Cikin kwanaki 100 na farko da zarar Atiku Abubakar ya hau karagar mulki zai bai wa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasar 'yancin cin gashin kansu," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Atiku ya ce da Bill Clinton yake koyi a siyasa

A cewarsa, 'za a yi ba sani, ba sabo, ko mai matsayin mutum, ba za a yi la'akari da jam'iyyar siyasarsa ba, kawai doka za a bi wajehjn yaki da cin hancin.

Ya ce daukacin manyan shari'o'in da ke gaban Hukumar Yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati ta EFCC an faro su ne a mulkin PDP, lokacin da Atiku yake mataimakin Shugaban kasa.

Don haka a cewar ofishin yakin nemansa zabensa, "Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza wajen yaki da cin hanci yadda ya kamata.