An kashe akalla mutum 15 a Zamfara

Jihar Zamfara na yawan fuskantar hare-hare 'yan bindiga

Asalin hoton, NIGERIAN ARMY

Wasu 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 15 a kauyen Magamin Diddi cikin yankin karamar Hukumar Muradun ta jihar Zamfara.

Bayanai sun ce 'yan bindigar sun auka kauyen ne bayan sallar azahar ranar Asabar, inda suka rika harbi kan mai tsautsayi.

Zuwa yanzu jami'an tsaro ko hukumomin jihar ba su ce komai game da wannan al'amari ba

Wani mutumin yankin ya ce mutanen kauyen da dama ne suka jikkata sakamakon harbe-harben da barayin suka yi tsawon lokaci ba tare da samun dauki daga jami'an tsaro ba.

Asalin hoton, AFP

Jihar Zamfara tana fama da hare-haren 'yan fashin shanu da masu satar mutane don neman fansa, wadanda suka tagayyara yanki.

Shaidan da BBC ta zanta da shi ya ce an kashe dansa na cikinsa da kuma jikansa a lokacin wannan hari.

"Akwai Iroro, wanda yake jikana ne sun harbe shi kuma bayan ya fadi suka bi shi suka yi masa yankan rago. Shi ma yana tare da abokinsa. Akwai wani Dan Yaya shi ko tafiya ma ba ya iya yi don ya samu matsala, amma sai da suka harbe shi. Shi kuma yarona yana gudu, suka taras da shi suka harbe," in ji shi.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya ce akwai 'yan gida daya, su hudu da aka harba, amma dai yana jin biyu suna nan ba su mutu ba.

A cewarsa sun tuntubi hukumomi don su kai wa 'yan garin dauki, amma dai har maharan suka gama abin da suka yi babu wani jami'in tsaro da ya je.

Shaidan wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce ranar Juma'a 'yan sa-kai sun je wani kauye a yankinsu inda irin wadannan barayi ke samun mafaka.

Inda suka je masallaci, suka samu wasu mutane da suke zargin barayi ne su uku suka kama, suka taho da su nan garin Magami, inda suka tsare su kafin jami'an tsaro su je su tafi da su.

Don haka, mutane na ganin wannan mai yiwuwa shi ya harzuka 'yan fashin, suka yiwo shiri suka kai musu harin ranar Asabar, in ji shi.

Jami'an tsaron da ke zaune a karamar hukumar Muradun sun yi nisa matuka da kauyensu wanda ba shi da kwalta.

Kafin a kai musu dauki gaskiya sai an dau lokaci tun da a bakin daji suke.

BBC ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, sai dai jami'in da ke magana da yawun 'yan sandan bai amsa kiran da aka yi ta yi masa ba.