'Cikin mako 2 an kashe mini mutum 40 a Tsafe'

Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto,

Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

'Yan fashi da kuma satar mutane don neman kudin fansa sun kashe akalla mutum 40 cikin mako biyu a yankin karamar hukumar Tsafe.

Hare-haren 'yan fashi a cikin jihar Zamfara na karuwa duk da matakan da hukumomin Najeriya ke cewa suna dauka da nufin murkushe su.

Ko a yammacin ranar Asabar sai da aka kashe akalla mutum 16 a kauyen Magamin Diddi na karamar hukumar Muradun.

Shugaban karamar hukumar Tsafe, Aliyu Abubakar Tsafe ya ce tsawon kwana uku ke nan 'yan bindigar na zuwa kauyen Asaula, inda rabin mutanensa suka tsere zuwa gudun hijira.

"Cikin daren Asabar sun sake komawa cikin garin Asaula, sauran mutanen da ke nan suka fatattake su, suka kashe hakimin garin, suka kona gidaje da amfanin gonan yawancin mutanen da suka gudu, in ji shi."

Haka kuma, duk a wannan dare sun kuma auka wa kauyen Sakiya, inda suka kashe mutane tare da sace mutum 11 ciki har mata guda uku.

Aliyu Abubakar ya ce kusan kowanne dare sai sun shiga gari daya zuwa biyu, su kashe mutane, su yi garkuwa da wasu, kuma su kona dukiyoyinsu.

A cewarsa: "Al'ummar wannan yanki, da yawansu sun bar garuruwansu. A yanzu haka, akwai 'yan gudun hijira sama da dubu biyu da muka ba su matsgunni a Tsafe, ban da wadanda suke gidajen 'yan'uwa da abokan arzuka."

Shugaban Tsafe ya ce kauyukan da hare-haren suka shafa sun hadar da Rugumawa da Doka da Bamma da Buke-buke da Kwadawa da Wailari da Enza da Fegin da kai.

Ya ce a bangarensu na jagororin al'umma suna aiki tare da jami'an tsaro wajen ba su gudunmawar da za su iya don gudanar da ayyukansu a tsawon shekara uku.

"Duk da haka nan, ba a samu nasara cikakka ba, wanda ya haifar da majalisar tsaro ta jihar Zamfara, muka fito da tsarin cewa za mu dauki matasa 'yan sa-kai wadanda za su taimaka wa jami'an tsaro ko kuma su taimaka wajen tsare garuruwansu."

"Wanda yake a kowacce karamar hukuma, mai daraja gwamna ya ba da umarni muka dauki wadannan mutane 500.

Ina tabbatar maka in ba don cikin taimakon Allah, da irin gudunmawar da irin wadannan 'yan sa-kai, da watakila abubuwan da ke faruwa yanzu, sai sun fi haka nan, in ji Aliyu Abubakar."

Shugaban karamar hukumar Tsafe ya ce a fahimtarsa jami'an tsaron da suke jihar Zamfara da makaman fadansu, sun yi kadan.