Zaki ya kashe Ba'amurkiya

A Lion

Asalin hoton, Getty Images

Wata matashiya 'yar Amurka ta gamu da ajalinta bayan wani zaki ya far mata a wani gandun daji da ke jihar North Carolina.

Kwana goma ke nan da matashiyar Alexandra Black 'yar shekara 22 ta fara aiki a cibiyar da ke Burlington, kafin wannan zaki ya kashe ta.

Zakin ya kubce ne daga dakin da aka killace shi lokacin da ake share kewayensa.

An harbe zakin ya mutu bayan kokarin sumar da shi ya ci tura.