Rundunar Sojin Najeriya za ta kwashe mutane daga Baga

Rundunar sojan Najeriya dai ta musanta cewa garin yana hannun 'yan Boko Haram din

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rundunar sojan Najeriya dai ta musanta cewa garin yana hannun 'yan Boko Haram din

Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya na cewa gwamnati da sojoji na yunkurin kwashe jama'ar da suka rage a garin Baga.

Saboda yakin da ake ci gaba da gabzawa tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram da suka shiga garin tun ranar Larabar makon jiya.

Sai dai bayanan da ke fitowa daga garin na cewa har yanzu akwai mutane da suka rage a garin na Baga, yayin da 'yan Boko Haram ke ci gaba da rike garin.

Rundunar sojan Najeriya dai ta musanta cewa garin yana hannun 'yan Boko Haram din.

Amma ta fitar da sanarwar cewa ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Borno wajen shirye-shiryen fitar da mutane daga Baga zuwa wasu wurare masu tsaro saboda ayyukan soji da ke faruwa a yankin.

Wani mazaunin Baga da a yanzu ya tsere daga garin ya shaida wa BBC cewa a jiya ne rundunar sojan ta fara tura motoci garin Baga domin dauke mutane zuwa birnin Maiduguri.

Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa an tura daruruwan sojoji garin duk da cewa dai babu wani fada da ke gudana a tsakanin bangarorin biyu.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai mayakan Boko Haram din suka shiga garin Baga kuma suka kafa tutarsu a babban masallacin garin bayan sun shafe sa'o'i suna fafatwa da sojoji da ke garin.

Sai dai bayan wannan harin, rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta murkushe hare-haren mayakan Boko Haram a garin Baga na jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Ibekunle Daramola ya fitar, ta ce bayan harin da mayakan Boko Haram suka kaddamar kan sojojin kasar, rundunar ta aika da jiragen yaki da suka fatattaki mayakan.