Hotunan yadda 'yan sanda suka zagaye gidan Dino Melaye

Titin Sangha, a nan ne gidan Dino Melaye yake
Image caption Titin Sangha, a nan ne gidan Dino Melaye yake

Tun a makon da ya gabata ne, 'yan sanda a Najeriya suka yi wa gidan Sanata Dino Melaye kawanya.

Sanata Melaye, shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta yamma a Najeriya.

'Yan sandan suna zarginsa ne da yunkurin kisan kai ga wani jami'in dan sanda mai suna Danjuma Saliu a ranar 19 watan Yulin bana.

Yanzu haka dai 'yan sandan suna nan sun kasa sun tsare inda suka bayyana cewa ba za su bar kofar gidan Sanatan ba har sai ya fito sun kama shi.

Ga wasu daga cikin hotunan abin da ke faruwa a kofar gidan Sanatan.

Image caption Lambar gidan Sanata Dino Melaye
Image caption Motar 'yan sanda sun tare kofar gidan Sanata Dino Melaye
Image caption 'Yan sanda suna sintiri a kofar gidan
Image caption Kofar gidan Sanata Dino Melaye