'Yan sanda sun kasa sun tsare a gidan Dino Melaye
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon yadda 'yan sanda suka kasa suka tsare a gidan Dino Melaye

Latsa alamar lasifika a sama domin kallon bidiyon

'Yan sanda sun shafe kwana hudu a kofar gidan Sanata Dino Melaye domin jiransa ya fito su kama shi.

'Yan sandan suna son ya je ne ya amsa tambayoyi kan zargin da ake ma sa na alaka da kisan wani dan sanda a ranar 19 ga watan Yuli.

Yanzu haka 'yan sandan suna nan sun kasa sun tsare inda suka bayyana cewa ba za su bar kofar gidan Sanatan ba har sai ya fito sun tafi da shi.